GORON JUMA’A 06-03-2026

[ad_1]

Jama’a barkanmu da shigowa wata mai alfarma watan Ramadan, barkanmu da sake kasancewa tare da wannan shafi na GORON JUMA’A. Shafi ne da yake bawa kowa damar miƙa saƙon gaishe-gaishensa, zuwa ga ‘yan’uwa da abokan arziƙi, na kusa da na nesa, har ma da waɗanda aka daɗe ba a haɗu ba. Kamar kowane mako, yau ma shafin na tafe da wasu saƙonnin gaishe-gaishen naku da kuka aiko mana kamar haka; Da farko ina mika gaisuwa ga Babban Editanmu Alhaji Bello Hamza da fatan yana cikin ƙoshin lafiya.

Saƙo daga Alaja Habibah Idris Jihar Sokoto:

Ina gaida Mahaifana Alhaji Idris Mai Kabewa, da Hajiya Lantana mai Goro, ina gaishe da ‘yan uwana maza da mata na gida dana waje. Ina gaida ƙawayena Zuby Hamza, Samira Yaƙub, Amina Garba, Taisir Ahmad, da fatan sun sha ruwa lafiya, sannan da fatan sun yi sallar juma’a lafiya

  • Nazari Kan Dabarun Shuka Mangoro A Zamanance
  • Yawan Cin Namijin Goro Na Hana Maza Haihuwa

Saƙo daga Awwal Amin Jihar Katsina:

Ina gaida Masoyiyata Fatima Yusuf Liman, ina gaida ƙannenta da yayyenta da mummynta gabaɗaya har da ƙawayenta, ni ne masoyinta mai ƙaunarta, har abada in sha Allah. Ina gaida abokaina Musa shanawa, Aminu Ak, Ibrahim mai hula da sauran ‘yan uwa na gida, Allah ya sa sun yi juma’a lafiya Allah ya bamu ladan Ibada.

Saƙo daga Abba Cele Jihar Kaduna:

Ina gaishe da Bilkisu Billy, ina gaishe da yayana Alhaji Hamisu mai walda Allah ya sa ka gama lafiya. Ina gaishe da babban abokina kuma amini na Salis Yusif, ina gaishe da abokaina na ko ina, da fatan za su yi juma’a lafiya.

Saƙo daga Hajiya Asma’u Lawan Jihar Kaduna:

Ina miƙa saƙo na zuwa ga ‘ya’yana Amina, da Hauwa, da Binta, da Zubaida, da Mu’allim, da Hassan da Hussaini da babban yayansu. Ina gaishe da masu adashi, ina gaishe da ƙawata Hajiya Murjanatu Ta Saraki, da yayyana, da sauran abokan arziƙi, Allah ya maimaita mana juma’a amin, a sha ruwa lafiya.

Saƙo daga Zeenat Idris Jihar Bauchi:

Ina miƙa saƙon Goron Juma’a ga dukkanin iyalanmu baki ɗaya, ina gaishe da al’ummar musulmin duniya, ƙawayena da saura ‘yan school ɗinmu, ƙannena da yayyena baki ɗaya, da fatan sun sha ruwa lafiya, kuma da fatan kowa zai yi kwalliyar juma’a tare da yin sallar juma’a lafiya.

Saƙo daga Aina’u Ibrahim Jihar Kaduna:

ina gaishe da Khaleed, Nauwara, Habibah, zulaihat, sajida da fatan za su yi juma’a lafiya, sannan kuma saƙon barka da shan ruwa zuwa ga ‘yan gidanmu da fatan kowa zai sha ruwa lafiya.

Saƙon daga Sa’id Ahmad Sa’id Jihar Katsina:

Ina gaida abokaina ina gaida mahaifana da ‘yan Club ɗinmu, ina gaida Aisha da Husnah, ina gaida Mujahid da Anwar da Saleem da fatan za su yi sallar Juma’a lafiya.

Saƙo daga Hajiya Talatu Munjibir:

Ina yi wa duk al’ummar musulmi na faɗin duniya barka da juma’a, kuma ina yi wa iyalaina barka da juma’a, da fatan kowa zai yi juma’a lafiya.

Saƙo daga Mamuda Al’amin Jihar Kaduna:

Ina gaida Yayata Fatima, ƙannen Farida, iyayena , ina yi wa kowa barka da juma’a.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *