Buƙatar Magance Matsalar Ƙarancin Abinci Mai Gina Jiki A Tsakanin Ƙananan Yara
[ad_1]
A bisa ƙoƙarin da ake yi magance ƙalubalen rashin abinci mai gina jiki musamman a tsakanin yara ƙanana da kuma ƙara ƙarafawa iyalai a ɗaukacin faɗin ƙasar nan guwai, hakan ya sanya, a kwnan baya, Sanata Remi Tinubu, mai ɗakin shugaban ƙasa,ta ƙaddamar da wani shiri na ƙasa, domin a magance wannan matsalar.
A jawabinta a yayin ƙaddamarwar Remi da alaƙanta wannan matsalar a matsayin gagarumar matsala wadda ake buƙatar a magance ta, matakin ƙasa, a ƙarƙashin wannan shirin.
- Shalƙwatar Tsaro Ta Ƙasa Na Shirin Gyaran Tsarin Tubabbun Ƴan Ta’adda
- Sin Ta Nemi Kasashen Duniya Su Hada Kai Wajen Magance Matsalolin Ilimin Yara A Yankunan Da Ake Fama Da Rikici
Shirin dai, za a fara wanzar da shi ne gadan-gadan a cikin watan Afirilun wannan shekarar, wanda kuma aka tsara shi musamman domin inganta samar da abinci mai gina jiki a tsakanin marasa ƙarfi da yara da shekarun su, suka faa daga shekaru shida.
A cewar Remi, za a gudanar da shirin ne a hukumomin kiwon kula da kiwon lafiya na farko da ke a ɗaukacin faɗin ƙasar, inda a nan ne, za gudanar da yin rijistar iyalan da aka zaɓo domin amfana da shirin.
Ta ƙara da cewa, waɗanda za su amfana, za a wayar masu da kai da kuma raba masu kayan abinici masu gina jiki da aka noma a ƙasar nan.
Taron ƙadamawar, ya samu halartar Sarakunan Gargajiya, Malaman Addini Ministan kiwon lafiya Farfesa Muhammad Pate ya sanar da cewa, kimanin yara ƙanana kaso 40 a cikin ɗari a ƙasar, na fuskantar matsalar ƙaramcin abinci mai gina jiki, wanda ya ce, wannann matsalar, na fara ne, tun kafin a haifi yaran.
A cewarsa, rashin abinci mai gina jiki, na ƙara haddasa mutuwar yara ƙanana, tun suna gakiyar tasowarsu, da hana su samun ingantaccen ilimi da fuskantar ƙalubale na dogon zango a rayuwarsu.
A bisa ra’ayin mu a wannan Jaridar yaƙar rashin abinci mai gina jiki a tsakanin yara ƙanana a ƙasar abu ne, da yake da matuƙar mahimanci, musamman duba da cewa, a duk makon farko na kowanne watan Agustan shekara, ana gudanar da faɗakarwa ta duniya kan mahimmancin shawar da jarirai Nonon Uwa.
Kazalika, tun kafin a fara fustantar ƙalubalen rashin tsaro a ƙasar, da kuma ɗimbin abincin da ake da shi a ƙasar, yara ƙanana na ci gaba da fuskantar ƙarancin abinci mai gina jiki.
A wasu shekarun baya, Asusun Tallafawa Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya wato UNICEF ta yi haɗaka da shirin samar da abinci wato RUTF na Gwamnatin Tarayya wa, musamman wannan shirin an samar da shi ne, yadda za a rinƙa yin amfani Gyɗar da aka sarrafa, domin magance babbar matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki a Arewacin Nijeriya.
Bugu da ƙari, shayar da Jarirai Nonon Uwa zalla, ya ci gaba da kasance kan aƙalla kaso 29 a cikin ɗari, a wan Agustan 2025, inda hakan ya nuna shayarwar, ta ragu da kaso 50 a cikin ɗari, kamar yadda Hukumar Kula da Kiwon Lafiya ta Duniya da Gwamnatin Tarayya, suka ayyana ana son a cimma
A cewar UNICEF, duk da cewa, mata masu shayarwa a ƙasar, sun ƙirƙiro da tsarin shayarwa da ya kao kaso 90 a cikin ɗari, amma har yanzu, ana ci gaba da kai wa wata shida na sahayar da Jarirai Nonon Uwa, wanda hakan ya nuna cewa, akwai buƙatar ƙara samar da tsare-tsare da bayar da goyon baya, a guraren yin aiki yadda mata ma’aikata masu shayarwa, za su samu ƙarin damar shayar da Jariransu, a wajen da suke yin aiki.
A shekaru da dama da suka gabata Gwamnatin Tarayya ta sha ƙiƙiro da ɗauki iri da ban da ban na magance ƙalubalen rashin abinci mai gina jiki, a tsakanin yara ƙanana, sai dai, Gwamnatin na samar da ɗaukin ne kawai, na wucin gadi.
Bugu da ƙari, wannan Jaridar za ta iya tunawa, a shekarar 2025, Gwmantin Tarayya ta ƙiriro da wani shiri na samar da abinci mai gina jiki wanda aka ƙaddamar, a ƙananan hukumomi 774 da ake da su a ƙasar.
Bayan wannan ƙaddamarwar, babban taro na ƙasa na samar sa abinci mai gina jiki da kuma samar da wadataccen abinci, ya biyo baya.
Taron, ya samu halartar ƙwararru daga fannoni da ban da ban, ministoci, hukumomin gwamnati, hukumomin tsaro, Sarakunan Gargajiya, ƴan majalisar taraya da majalisun dokkki da sauran abokan haɗaka.
Mataimakin Shugaban Ƙasa Sanata Kashim Shettima, wanda ya ƙaddamar da buɗe taron ya buƙaci, da samar da dabarun ƙara inganta samar da abinci mai gina jiki da kuma wadataccen abinci a ƙasar.
Sai dai, batun, ba wai kawai halartar Sarakunan Gargajiya da Mlaman Addainai waje ƙaddamarwa bane, akwai kuma matuƙar buƙatar, su ƙara zage damtse wajen faɗaɗar da alumomin su, kan mauhimmancin ciyar da yara ƙanana abinci, mai gina jiki, duba da cewa, ana samun koma baya, wajen ciyar da yaran, waɗanda sune, manyan gobe.
Wannan Jaridar na yin la’akari da cewa, ko da yake kundin tsarin mulkin ƙasar na 1999 da aka sabunta, bai bai wa Sarakunan damar bayar da wata gudunmawa ba, amma suna taimaka wa, wajen wanzar da zaman lafiya da warware rikice-rikice.
Daga watan Afirilun 2025, bisa wasu rahoton da Bankin Duniya ya fitar, sun nuna cewa, aƙalla ƴan Nijeriya kaso 75.5, na ci gaba da zaman cikin talauci.
Bugu da ƙar, yawan masu zama a cikin talauci a karkara, sun ruɓanya yawan mazauna a birne, inda a karkara, ake da kaso 41.3.
Bisa bincken kiwon lafiya da aka gudanar daga 2023 zuwa 2024 na NDHS da kuma fashin baƙin da aka yi a kwanan baya kan ƙarancin abnci mai gina jiki, daga 2024 zuwa 2025, hakan ya nuna cewa, yara ƙanana ƴan shekaru ƙasa da biyar da ke fama da ƙarancin abinci maras jina jiki, da ke zaune a karkara, sun kai sama da kaso 50.
Akwai kuma buƙatar Sarakunan Gargajiya, su rinƙa faɗaɗar musamman mata, kan mahimmancin shayar da Jarirai, Nonon Uwa.
Sai dai, abin damuwar mu shi ne, hujjoji da dama a baya sun nuna cewa, irin wannan ɗaukin da ake samarwa, a ƙarshe, ana yin watsi da shi ne, ba tare da waɗanda ake da burin su amfana ba, sun ci gajiyar ɗaukin ba.
A ƙasar nan, ba wai an gaza samar da tsare-tsare bane, amma matsalar itace, rashin wanzar da tsare-tsaren, yadda ya kamata.
A kwanan baya, an ruwaito shugaba Bola Tinubu ya sanar da cewa, ana samar da ingantacciyar kiwon lafiya, hakan ne zai sanya, a samar da yara manyan gobe, wajen gina ƙasa.
A lokacin yana raye, tsohon shugaban ƙasar Amurka John F. Kennedy, ya bayyana cewa, yara sune babban ginshiƙin yari, a duk faɗin duniya kuma waɗanda ake da babban fana, samar masu
da gobe, mai kyau.
[ad_2]
Source link