Japan za ta bai wa Najeriya rancen $190m don inganta wutar lantarki

[ad_1]



Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu, ya bayyana cewa Najeriya za ta karɓi rancen dala miliyan 190 daga Ƙasar Japan domin inganta wutar lantarki.

Wannan na cikin wata sanarwa da ma’aikatar lantarki, yayin da ake gudanar fa taron ƙasashen Afirka da ke gudana a birnin Yokohama na Ƙasar Japan.

Tawagar Najeriya ƙarƙashin Shugaba Bola Tinubu ta halarci taron.

Rancen zai fito ne daga hukumar Japan International Cooperation Agency (JICA), kuma ana sa ran zai taimaka wajen samar da wutar lantarki mai ɗorewa a yankunan da ba su da isasshiyar wuta.

Ma’aikatar ta kuma ce wannan lamuni ya zo ne a matsayin ƙari ga wani tallafi na dala miliyan 750 daga Bankin Duniya ƙarƙashin shirin Mission 300 Compact.

Tallafin na da nufin samar da wutar lantarki mai ɗorewa ga mutane aƙalla miliyan 17 a Najeriya.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *