Binciken CGTN: Fiye Da 90% Na Masu Amfani Da Intanet A Duniya Sun Yi Tir Da Harin Amurka Da Isra’ila A Iran

[ad_1]

A ranar 28 ga watan Fabrairu ne Amurka da Isra’ila suka kaddamar da harin soji na hadin gwiwa kan kasar Iran, wanda ya yi sanadin mutuwar jagoran addini na kasar Ayatollah Ali Khamenei. A wani mataki na ramuwar gayya, Iran ta kai hari kan sansanonin sojin Amurka da dama a yankin Gabas ta Tsakiya da kuma wuraren da ke da alaka da Isra’ila, lamarin da ya kara ta’azzara halin da yankin yake ciki.

Wata kuri’ar jin ra’ayoyin jama’a ta shafin intanet da CGTN ta gudanar a tsakanin masu amfani da shafukan intanet a duniya ta nuna cewa kashi 93.9% na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu sun yi tir da matakin sojin Amurka da Isra’ila, inda suke ganin hakan ya saba wa ‘yancin kai, tsaro, da kuma keta hurumin yankunan kasar Iran.

An dauki wannan matakin na soja ne a yayin da ake kan tattaunawar diflomasiya tsakanin Amurka da Iran, lamarin da ya yi matukar girgiza al’ummar duniya matuka. A cikin binciken jin ra’ayoyin, kashi 86.8% na masu bayyana ra’ayoyi sun soki Amurka game da tsaurara matakan soja a yayin tattaunawar, suna ambatar hakan da “babakeren Amurka.”

Kashi 90% na masu bayyana ra’ayoyin kuma sun bayyana damuwarsu kan cewa shirin zaman lafiyar yankin Gabas ta Tsakiya da ya riga ya shiga halin-ha’ula’i zai kara tabarbarewa cikin sauri, suna masu amannar cewa kara rura wutar rikici a yankin Gabas ta Tsakiya ba zai biya bukatar ko wane bangare ba. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *