Wane Ne Ayatollah Ali Khamenei, Jagoran Addinin Iran?

[ad_1]

Ayatollah Ali Khamenei shi ne jagoran addini mafi girma a ƙasar Iran, kuma mutum na biyu da ya riƙe wannan muƙami tun bayan juyin juya-halin Musulunci da aka yi a shekarar 1979.

Ya hau kan madafun iko ne a shekarar 1989 bayan rasuwar jagoran juyin juya-halin ƙasar, Ayatollah Ruhollah Khomeini, kuma tun daga lokacin yake jagorantar al’amuran addini da siyasar ƙasar.

  • Ɗalibai Miliyan 1.5 Ne Suka Yi Rajistar Jarrabawar UTME 2026
  • Shawarwari 40 Zuwa Ga Uwargida (1)

Yawancin matasan Iran sun taso ne suna ganinsa a matsayin babban jagoransu na addini da kuma wanda ke da ikon yanke hukunci kan manyan batutuwan ƙasa.

A tsarin mulkin Iran, jagoran addini na da faɗa a ji matuƙa, domin yana da ikon amincewa ko dakatar da manyan manufofin gwamnati, tare da damar naɗa manyan jami’an gwamnati da na tsaro.

Haka kuma shi ne babban kwamandan rundunonin sojin Iran, ciki har da dakarun juyin juya-hali na ƙasar da ake kira Iranian Revolutionary Guard Corps (IRGC).

An haifi Khamenei ne a shekarar 1939 a birnin Mashhad, wanda ke daga cikin manyan biranen Iran. Ya fito ne daga gidan malamin addinin Shi’a, kasancewar mahaifinsa malami ne mai koyar da ilimin addini.

Tun yana ƙarami ya fara koyon karatun Alƙur’ani da ilimin addini, har ya fara koyarwa yana kusan shekara 11 a duniya.

Khamenei ya shahara wajen sukar gwamnatin Shah ta Iran kafin juyin juya-halin 1979, lamarin da ya sa aka riƙa tsare shi sau da dama tare da fuskantar wahalhalu a gidan yari.

Bayan nasarar juyin juya-halin Musulunci, an naɗa shi babban limamin Juma’a na birnin Tehran, kafin daga bisani a zaɓe shi shugaban ƙasar Iran a shekarar 1981.

A shekarar 1989 kuwa, majalisar malaman addini ta Iran ta zaɓe shi a matsayin jagoran addini mafi girma domin maye gurbin Ayatollah Khomeini bayan rasuwar na farkon.

A yau, ana kallon Ayatollah Ali Khamenei a matsayin mutum mafi tasiri a siyasa, tsaro da kuma tafiyar addini a Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *