HOTUNA: Zanga-zangar kisan Khamenei ta ɓarke a Pakistan

[ad_1]



Rahotanni na cewa ana ci gaba da zanga-zangar adawa da Amurka a birnin Karashi na ƙasar Pakistan.

Wannan na zuwa ne biyo bayan hare-haren haɗin gwiwar da Amurka da Isra’ila suka kai Iran a ranar Asabar, wanda ya yi ajalin jagoran addini na ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei.

Yadda jami’an tsaro ke faɗi tashi da masu zanga-zanga a Pakistan.
Hoto: AP

Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito cewa aƙalla mutum takwas ne suka mutu a zanga-zangar goyon bayan Iran da aka gudanar a kusa da ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Karachi.

Kakakin Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa na yankin, Muhammad Amin ya shaida wa AFP cewa mutum 20 ne suka jikkata yayin zanga-zangar.

Wasu rahotonni sun bayyana cewa jami’an tsaron Amurka da ke harabar ofishin jakadncin ne suka buɗe wuta kan masu zanga-zangar, sannan daga baya ’yan sandan Pakistan suka harba yahaƙi mai sa hawaye.

A cewar AFP wasu fusatattun matasa ne suka haura katangar domin shiga harabar ofishin jakadancin yayin da wasu suka karya tagogin ginin.

Bidiyoyin da aka yaɗa sun nuna yadda matasan suka riƙa karya tagogin.

Dubban mutane suka fantsama kan titunan Lahore da Skerdi, domin guidanar da zanga-zangar, yayin da ake sa ran yin zanga-zangar a kusa da ofishin jakadancin Amurka da ke Islamabad, babban birnin ƙasar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *