Shalƙwatar Tsaro Ta Ƙasa Na Shirin Gyaran Tsarin Tubabbun Ƴan Ta’adda
[ad_1]
Shalƙwatar Tsaro ta Ƙasa (DHQ), ta bayyana cewa ana nazarin shirin gyara da sauya tunanin ‘yan ta’adda da suka miƙa wuya domin daidaita shi da halin da ake ciki a yanzu.
Daraktan Yaɗa Labaran rundunar tsaron, Manjo Janar Micheal Onoja, ya ce shirin Operation Safe Corridor wanda aka ƙaddamar tare da gwamnatin Jihar Borno da ma’aikatun tarayya, ya samu nasarori a farko, amma ya fuskanci ƙalubale da ke buƙatar sake dubawa.
- Wata Uku Da Kafa Dokar Ta-ɓaci: Har Yanzu Matsalar Tsaro Na Ci Gaba Da Ta’azzara
- Direbobi Sun Koka Kan Dawowar Matsalar Tsaro Kan Babbar Hanyar Damaturu Zuwa Biu
Ya jaddada cewa duk da laifukan da mayaƙan Boko Haram suka aikata, har yanzu ‘yan ƙasa ne, don haka idan akwai damar gyara su ta hanyar doka, ya kamata a yi la’akari da hakan, yana mai cewa nan ba da jimawa ba za a sanar da sabbin matakan aiki na shirin.
DHQ ta kuma tabbatar da cewa taimakon da Amurka ke bai wa Nijeriya kan yaƙi da ta’addanci kyauta ne, ba tare da ya tauye ikon ƙasa ko ‘yancinta ba, tare da bayyana cewa jami’an Amurka da suka iso ƙasar suna nan ne domin horaswa da ƙarfafa dabarun yaƙi.
Onoja ya buƙaci kafafen yaɗa labarai su rika bayar da rahotannin tsaro cikin kishi da kulawa, yana mai cewa yawan yaɗa labaran hare-haren ta’addanci kan iya taimaka wa masu aikata su wajen yaɗa fargaba.
[ad_2]
Source link