Yara 700,000 ne ba sa zuwa makaranta a Najeriya – Gwamnati
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa, yara sama da 700,000 a faɗin Najeriya ba sa zuwa makaranta a halin yanzu, inda ta yi kira ga gwamnatoci a kowane mataki da su ɗauki matakin gaggawa na haɗin gwiwa domin magance wannan matsala.
Sakataren Zartarwa na Hukumar Kula da Almajirai da Ilimin Yara da ba sa zuwa makaranta (NCAOOSCE), Dakta Muhammad Idris, ne ya bayyana wannan adadi a taron ƙoli na farko kan ilimin bai-ɗaya na jihar Benuwe da aka gudanar a Makurdi.
Ya bayyana halin da ake ciki a matsayin abin damuwa da ke buƙatar ɗaukar matakin gaggawa.
Idris ya ce bayanan sun nuna girman giɓin ilimi a faɗin ƙasar, inda ya yi kira ga jihohi da su ɗauki matakan da suka dace domin tabbatar da cewa an sa yaran da suka kai shekarun makaranta kuma aka ci gaba da riƙe su a makarantun firamare.
Taron, wanda Hukumar Ilimin Bai-ɗaya ta Jihar Benuwe (SUBEB) ta shirya tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Bai-ɗaya ta ƙasa (UBEC), NCAOOSCE, da kamfanin Uniɓersal Learning Solutions (ULS), ya mayar da hankali kan hanyoyin zamani na ƙara yawan ɗalibai da kuma tabbatar da zama a makarantun firamare.
Matakan da Jihar Benuwe ta ɗauka
Gwamna Hycent Alia ya ƙaddamar da shirin ‘Brace Up Project’ kuma ya ƙaddamar da jami’an sa ido na ɗalibai a ƙananan hukumomi 23 domin gano yara da kuma sa ido kan waɗanda ba sa zuwa makaranta.
Ya bayyana cewa: Tuni aka gano yara 525 da ba sa zuwa makaranta a jihar.
An dawo da su tsarin karatu tare da ba su kayan makaranta kyauta.
Gwamnati za ta ci gaba da gangamin neman yara har sai an tabbatar dukkan yaran da abin ya shafa sun dawo makarantu.
Haka kuma, Sakatariyar Zartarwa ta UBEC, Hajiya Aisha Garba, ta ce gyare-gyaren da hukumar ta yi ya bai wa jihohi damar samun sama da Naira biliyan 100 na kuɗin tallafi domin ƙarfafa bayar da ilimin bai-ɗaya.