NAJERIYA A YAU: Me Nadin Sabon Sufeton ‘Yansanda Ke Nufi Ga Tsaron Cikin Gida Najeriya?

[ad_1]

Ƙarin Podcasts



Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa sabon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (IGP), matakin da ya sake jawo hankalin al’umma kan makomar tsaro da gyaran harkokin rundunar ‘yan sandan ƙasar nan. Naɗin sabon jagoran rundunar ya zo ne a daidai lokacin da ake fuskantar ƙalubale daban-daban na tsaro, ciki har da satar mutane, ta’addanci, da rikice-rikicen cikin gida a wasu sassan ƙasa.

Sabon Sufeton ana sa ran zai ɗora kan nasarorin da aka samu a baya tare da kawo sababbin tsare-tsare da dabarun da za su ƙarfafa yaƙi da laifuka, inganta hulɗa tsakanin ‘yan sanda da al’umma, da kuma farfaɗo da martabar rundunar.

Ko ta yaya wannan naɗin sabon shugaban ‘yansandan zai amfani tsaron cikin gida Najeriya?

Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.

Domin sauke shirin, latsa nan


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *