’Yan bindiga sun kashe mutum 5 a Masallaci a Kebbi
[ad_1]
Wasu ’yan bindiga da ake zargin Lakurawa ne, sun kai hari cikin wani masallaci da ke garin Dadinkowa, a Ƙaramar Hukumar Maiyama a Jihar Kebbi, inda suka kashe mutum biyar tare da jikkata wasu biyar yayin suke tsaka da sallah.
Wani mutum da gidansa ke jikin masallacin ya ce maharan sun shigo garin ne a ɓoye, tare da kashe fitilun baburansu, a daren ranar Laraba.
Ya ce bayan sun leƙa cikin masallacin suka ga mutane na sallah ba tare da wani makami ba, sai suka buɗe musu wuta.
“Nan take suka kashe mutum biyar, wasu biyar kuma suka jikkata. An kai waɗanda suka ji rauni asibiti,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa ana jin ƙarar harbe-harbe, take jama’a suka dinga tserewa daga masallacin domin tsira da rayukansu, yayin da ’yan bindigar suka ci gaba da harbi a iska kafin su bar garin.
A cewarsa, maharan ba su zo da niyyar yin garkuwa da kowa ba, sun kashe mutanen sannan suka tafi.
Ya ce ana zargin harin na da alaƙa da ramuwar gayya kan wasu hare-haren da aka ce sojoji sun kai musu a yankin.
Bayan faruwar lamarin, jami’an tsaro ciki har da sojoji da ’yan sanda sun isa garin domin tabbatar da tsaro.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Bashir Usman, bai samu ɗaga waya ba domin jin ta bakinsa kan faruwar harin.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link