Kotu Ta Sanya Ranar 23 Ga Afrilu Don Sauraron Shari’ar El-Rufai Kan Zargin Kutse A Wayar Ribadu

[ad_1]

Kotun Tarayya da ke Abuja ta ɗage shari’ar tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, zuwa ranar 23 ga watan Afrilu, 2025.

Hukumar DSS ce ta shigar da tuhume-tuhume guda uku, ciki har da zargin yin kutse a wayar Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkar Tsaro (NSA), Nuhu Ribadu.

  • Gwamnatin Tarayya Ta Ce Ba Ta Taɓa Goyon Bayan Musguna Wa Kiristoci Ba
  • ‘Yan Majalisar Dokokin Adamawa 6 Sun Fice Daga Jami’yyar PDP

El-Rufai ya bayyana a wata hira da ya yi da gidan  talabijin na Arise cewa shi da wasu sun saurari wayar Ribadu, kan yadda ya bayar da umarnin a kama shi.

El-Rufai bai halarci zaman kotun na ranar Laraba ba saboda har yanzu yana hannun ICPC, inda suke bincike kan zargin almubazzaranci da kuɗaɗe.

Tuni hukumar ta kama wani na kusa da El-Rufai da ake tuhuma da hannu a lamarin.

Kotun za ta ci gaba da sauraron shari’ar a ranar da aka saka bayan kammala binciken El-Rufai.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *