DSS ta kama mutum na 6 da ake zargi da kitsa harin Owo




Hukumar Tsaro ta Farin Kaya DSS ta sanar da cafke wani mutum da ake zargi yana da hannu a harin da aka kai cocin Katolika na St. Francis da ke Owo a Jihar Edo a shekarar 2022.

Mutumin nan bayan nan wanda aka bayyana da suna Sani Yusuf, shi ne cikon na shida da ake zargi da kitsa harin wanda ya yi sanadiyar mutuwar fiye da masu ibada 40 tare da jikkata wasu da dama.

Tuni dai hukumar DSS ta riga ta kama mutum biyar waɗanda suke fuskantar shari’ar aikata laifukan ta’addanci.

Gidan Talabijin na Najeriya NTA ya ruwaito cewa, Sani Yusuf, ya shafe kusan shekara huɗu yana ɓuya kafin a kama shi a wata unguwa mai suna Iguosa da ke Ƙaramar Hukumar Ovia North a Jihar Edo.

Wata majiyar tsaro ta bayyana cewa Yusuf wani babban kwamanda ne a ƙungiyar ISWAP kuma bayan harin Owo ya tsere zuwa Kano kafin daga bisani ya koma ɓuya a yankin na Edo.

Rahotanni sun ce ya amsa laifin yana da hannu a harin da aka kai cocin da kuma wasu hare-haren ƙungiyar, ciki har da farmakin da aka kai a barikin sojoji na Suleja a watan Yulin 2022 da kuma sace-sacen mutane a Kaduna da kewaye.

“Ya kuma amince yana da hannu a harin da aka kai a shingen sojoji na Zuma Rock kusa da Suleja, wanda ya yi sanadin mutuwar sojoji biyar.

“Haka kuma ya bayyana cewa ya taɓa aiki a ƙarƙashin wani babban jagoran ƙungiyar mai suna Abu Ikirimah wanda aka kama a 2024,” in ji majiyar da NTA ta ruwaito.

Jami’an tsaro sun ce kama Yusuf wani gagarumin ci gaba ne a ƙoƙarin tabbatar da adalci ga waɗanda harin ya rutsa da su, da kuma ƙara tabbatar da yaƙi da ta’addanci a faɗin Najeriya.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *