Ramadan: Remi Tinubu Ta Bayar Da Gudummawar Buhun Shinkafa 700 Ga Babban Masallacin Abuja

[ad_1]

Uwargidan Shugaban Kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bayar da gudummawar buhun shinkafa sama da 700 ga Masallacin Kasa da ke Abuja, domin rabawa Musulmai mabukata mazauna Babban Birnin Tarayya (FCT), Abuja.
Gudummawar, wacce aka bayar a ƙarƙashin Shirin Sabunta Fata (RHI) na Ofishin Uwargidan Shugaban Kasa, an yi shi ne don tallafawa Musulmai masu azumi a cikin watan mai tsarki da kuma rage wa magidanta matsin tattalin arziki da suke fuskanta.
  • Darussa Daga Ramadan Na 6: Girmama Ni’ima Da Gujewa Almubazzaranci A Ramalana
  • An Wallafa Mukalolin Xi Kan Fahimtar Ayyukan Shugabanci
Da yake gabatar da kayayyakin a madadin Uwargidan Shugaban Kasa a ranar Litinin, shugaban Kwamitin Jin Daɗin Masallacin Kasa, Malam Abubakar Sadiq, ya nuna godiyarsa ga wannan alherin, yana mai bayyana shi a matsayin wanda yazo a kan lokaci.
An raba shinkafar ga zawarawa, marayu, da sauran ƙungiyoyin dake tallafawa masu rauni a faɗin Babban Birnin Tarayya.
An gudanar da aikin rarrabawar ne a cikin harabar masallacin jim kaɗan bayan sallar Zuhur, inda waɗanda suka amfana suka nuna farin ciki da godiya ga wannan alherin na Uwargidan Shugaban Kasa.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *