Atiku ya bayyana fargaba kan halin da El-Rufai yake ciki
[ad_1]
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma jigo a jam’iyyar haɗaka ta ADC, Atiku Abubakar, ya bayyana damuwa mai tsanani kan tsare tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, yana mai cewa iyalansa da abokansa na cikin fargaba game da lafiyarsa da walwalarsa.
Atiku, a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, ya ce dole ne Gwamnatin Tarayya ta fito ta fayyace wace hukuma ce ke tsare da El-Rufai — ko dai EFCC, ICPC, DSS ko wata hukumar tsaro ta daban.
A cewarsa, ɓoye bayanai kan irin wannan lamari na tsare mutum na ƙara haifar da shakku a zukatan jama’a, alhali Kundin Tsarin Mulki ya ba ’yan ƙasa haƙƙin sanin gaskiya.
Ya jaddada cewa duk hukumar da ke da alhakin tsare El-Rufai tana da nauyin kare tsaronsa, mutuncinsa, da tabbatar masa da kulawar lafiya, tare da ba shi damar ganawa da iyalansa da lauyoyinsa.
Atiku ya ce rahotannin da ke cewa El-Rufai na fama da zubar jini ta hanci, tare da zargin hana iyalansa ganinsa, abin damuwa ne ƙwarai wanda ba ya kan doron tsarin dimokuraɗiyya.
Ya ƙara da cewa idan hukumomi ba za su iya tabbatar da lafiyarsa da duk wani haƙƙinsa ba, to abin da ya dace bisa doka da jin ƙai shi ne a ba shi beli ba tare da ɓata lokaci ba.
“Idan wani abu ya faru da shi, alhakin hakan zai rataya a wuyan gwamnati,” in ji Atiku.
Ya gargaɗi Gwamnatin Najeriya da ta ɗauki wannan lamari da muhimmanci, tare da kiran a kawo ƙarshen duk wani yanayi da zai iya jefa lafiyar El-Rufai cikin haɗari.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link