“’Yan bindiga na cikin mawuyacin hali sakamakon ɓullar cuta a Neja da Zamfara”
[ad_1]
Rahotanni daga Jihohin Neja da Zamfara, na nuna cewa ɓullar wata cuta a tsakanin ’yan bindiga ta fara rage ƙarfinsu na kai hare-hare da satar mutane.
Hakan na faruwa ne saboda ƙarancin kuɗi, abinci da magunguna a sansanoninsu.
Wata majiya ta ce halin da ake ciki a sansanonin maharan ya ta’azzara, lamarin da ya rage ƙarfinsu na kai wa al’umma hare-hare.
Wani mutum da ya tsere daga hannun ’yan bindiga a Jihar Neja kuma ya nemi a ɓoye sunansa, ya bayyana matsalolin rashin lafiya a matsayin mummunan yanayi da ya fantsama a sansanin.
Ya ce fursunoni da wasu daga cikin ‘yan bindigar na fama da cututtuka.
Ya ƙara da cewa rashin magunguna da kulawa a cikin daji na ƙara tsananta halin da suke ciki, inda mutane da dama ke cikin mummunan yanayi.
“Na kwashe kwanaki cikin tsoro, ina fargabar kamuwa da cutar da ke yaɗuwa a tsakaninsu saboda babu magunguna ko kulawar likita,” in ji shi.
Ya ƙara da cewar akwai buƙatar jami’an tsaro su ƙara ƙaimi wajen kai musu farmaki.
“Idan jami’an tsaro suka ƙara ƙoƙari a yanzu, akwai yiwuwar a ƙara raunana su, ganin irin halin da suke ciki,” in ji shi.
Da yake magana kan lamarin, masani kan harkokin tsaro Usman Bala Tsamiya Babba, ya ce wannan na nuna tasirin ci gaba da ɗaukar matakan tsaro da ake yi.
Ya ce toshe hanyoyin da ake bi wajen kai musu abinci, magunguna da kuɗi zai iya rage tasirinsu sosai.
“Idan aka datse hanyoyin da suke samun kayayyaki, hakan na iya na kawo ƙarshen ayyukansu,” in ji shi.
Masanin ya kuma buƙaci gwamnati ta ƙara ƙaimi wajen magance matsalar tsaro a yankunan da abin ya shafa, yana mai jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da al’umma.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link