Gwamnatin Tarayya Da Gwamnonin APC Sun Ba Da Gudummawar Naira Biliyan 8 Ga ‘Yan Kasuwar Singa
[ad_1]
Gwamnatin tarayya ta sanar da bayar da tallafin naira biliyan 5 ga wadanda suka hadu da iftila’in gobara a kasuwar Singa da ke Jihar Kano a kwanakin baya.
Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ne ya bayyana hakan, a ranar Litinin a wata ziyarar jaje da ya kai kasuwar, inda aka yi asarar dukiyoyi da dama na biliyoyin naira a gobarar da ta tashi a ranar Asabar.
- Mutane Da Dama Sun Mutu, Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Sokoto
- Ramadan: Lokutan Buda-Baki Da Sahur Na Azumi Na 2
Shettima, wanda ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici da ya shafi kasa ya ce; rashin ba Jihar Kano kadai ya shafa ba, har ma da kasa baki-daya.
Sannan ya yi addu’a ga wadanda abin ya shafa, ya kuma roki Allah da ya kawar mana da bala’o’i kowane iri a nan gaba.
A yayin ziyarar, mataimakin shugaban kasar ya samu rakiyar gwamnonin Jihohin Jigawa da Kebbi da kuma Imo.
Shugaban kungiyar dillalan Kasuwar ta Singa, Junaid Zakari ya yaba wa gwamnatin tarayya, bisa abin da ya kira da daukar matakin da ya dace a kan lokaci cikin karamci.
A halin da ake ciki yanzu kuma, Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kuma bayyana cewa; gwamnonin jam’iyyar APC, sun bayar da gudunmawar naira biliyan uku ga wadanda gobarar ta shafa.
Haka zalika, ya tabbatar da bayar da tallafin ne a lokacin da yake jawabi a wajen sauya shekarsa zuwa jam’iyyar a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano.
Ya kuma bayar da tabbacin cewa, za a yi amfani da kudaden cikin adalci, wajen tallafa wa ‘yan kasuwar da abin ya shafa da kuma farfado da harkokin kasuwanci a kasuwar.
Gobarar dai, ta kona shaguna sama da 1,000 a babbar cibiyar hada-hadar kayayyakin kayan masarufi ta Arewacin Nijeriya.
Hukumomin kashe gobara sun ce, suna ci gaba da gudanar da bincike, domin gano musabbabin tashin gobarar da kuma Barnar da ‘yan kasuwar suka yi.
[ad_2]
Source link