Lakurawa sun kashe mutane 33 a Jihar Kebbi — ’Yan sanda
[ad_1]
Rahotanni daga Jihar Kebbi na cewa ’yan ta’addar Lakurawa sun kashe mutane sama da 30 a wasu hare-hare da suka kai wa wasu ƙauyukan jihar bakwai.
Kakakin ’yan sandan Jihar Kebbi, SP Bashir Usman ya ce lamarin ya faru a yankin Bui, Ƙaramar Hukumar Arewa a yammacin ranar Laraba, kuma tuni aka tura jami’an tsaro domin bin bayan ’yan ta’addar.
Bashir ya ce haɗin gwiwar sojoji da sauran jami’an tsaro an baza su wuraren don dawo da kwanciyar hankali.
“Muna baƙin cikin rasa rayukan mutane 33 da ba su ji ba su gani ba, kuma muke miƙa ta’aziyarmu ga iyalan marigayan da mutanen Ƙaramar Hukumar Arewa gaba ɗaya.”
Ya ce a binciken da aka yi an tabbatar da ’yan bindigar Lakurawa ne suka shiga yankin domin satar shanu, daga yankin ƙaramar hukumar Gudu a Sakkwato.
Mutanen ƙauyen Mamunu, Awasaka, Tungan Tsoho, Makangara, Kanzo, Gorun Naidal, da Dan Mai Ago sun haɗu don kare kansu a lokacin da maharan suka kawo farmakin amma ɓata-garin suka hallaka mutane 33 a cikinsu.
Ya ce akwai buƙatar cigaba da aiki tare a tsakanin jami’an tsaro kan waɗannan hatsabiban ’yan bindiga.
Ya nemi fararen hula da su riƙa ba da bayanin duk wani motsi da ba su yarda da shi ba, ga jami’an tsaro su daina tunkarar ’yan bindigar kai tsaye, saboda hakan na da hatsari.
Ya ce hukumar tana tsaye sai ta tabbatar da kawar da ɓata-garin da masu taimakon su.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link