Hukumar Shari’ah Ta Kare Zargin Da Amurka Ke Yi Wa Kwankwaso

[ad_1]

Majalisar Koli ta Shari’a a Nijeriya (SCSN), ta yi watsi da ikirarin da aka yi a cikin wani kudiri na baya-bayan nan a gaban Majalisar Dokokin Amurka, kan zargin kisan kiyashin Kiristoci a Nijeriya, inda ta bayyana labarin a matsayin na karya mai kuma matukar hadari.

A wata sanarwa da ta fitar dauke da sa hannun babban sakatarenta, Nafiu Baba Ahmad, majalisar ta kuma yi Allah wadai da abin da ta bayyana a matsayin hari ga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dangane da wannan zargi.

  • SAHUR (Falalarsa Da Fa’idojinsa) Na 3
  • Mutane Da Dama Sun Mutu, Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Sokoto

Majalisar ta ce, yayin da Nijeriya ke fuskantar manyan kalubalen tsaro da suka hada da ta’addanci da na ‘yan ‘yan bindiga da kuma tashe-tashen hankula da suka hada da muggan laifuka, babu matsayi da gwamnati ko kuma wani addini ke kokarin dauka, domin kawo karshen kiristoci.

Hukumar ta SCSN, ta yi suka kan abin da ta kira yadda ake dogaro ga sharhohin da ba a tabbatar da su ba, da kuma bayanan da ba a tantance su ba, tana mai cewa; ya kamata manyan da suke yanke shawara na kasa da kasa, su kasance suna amfani da sahihin bincike da cudanya da cibiyoyin ilimi.

Dangane da maganar da aka fada a kan Kwankwaso a tsarin majalisar dokokin Amurka, majalisar ta bayyana hakan ne a matsayin rashin adalci, inda ta ce; zaBen mutum daya a cikin ‘yan siyasar Nijeriya, na nuna matukar son kai maimakon yin adalci.

Ya ce, babban kalubalen da Nijeriya ke fuskanta shi ne, na taBarBarewar tattalin arziki da kuma gazawar shugabanci da suka haifar da fatara da rashin tsaro, inda ta bukaci masu lura da al’amura da su mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi tsarin mulki, maimakon yi wa daidaikun mutane zagon kasa.

Majalisar ta ci gaba da cewa, adawar da Kwankwaso ya yi na ayyana Nijeriya a matsayin kasa ta musamman (CPC), bisa zargin cin zarafi da ake yi wa addini, na iya haifar da abin da ta kira  a matsayin“bi ta da kulle”.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *