Jerin Sharuddan Da Chelle Ya Gindayawa NFF Domin Cigaba Da Jagorantar Super Eagles

[ad_1]

A wani rahoto da Leadership Hausa ta tattato daga sauran jaridun cikin Gida, kocin babbar tawagar kwallon kafa ta Nijeriya (Super Eagles) Eric Chelle ya gindaya wasu sharudda ga hukumar kwallon kafa ta Nijeriya NFF matukar anason ya cigaba da kasancewa a matsayinsa na kocin Super Eagles, daga cikin sharudda 19 da tsohon kocin na tawagar kwallon kafa ta kasar Mali ya gindaya akwai karin albashi.

A yan kwanakinnan and danganta Chelle da komawa kungiyar kwallon kafa ta Olympic Marseille ta kasar Faransa, amma hakarsa bata cimma ruwa ba bayan kungiyar dake buga gasar Ligue 1 ta nada sabon koci, Eric Chelle ya sanya hannu kan kwantiragin shekaru biyu da NFF a watan Janairun shekarar 2025 tare da karin shekara daya idan yayi aikin mai kyau.

A cewar yar jaridar wasanni, Shina Oludare, kocin wanda yakeda shaidar dan kasa ta kasashe biyu ( Faransa da Mali) ya gabatar da sharudan da aka gabatar ga NFF a ranar 22 ga watan Janairun shekarar 2026, bayan abin da ya bayyana a matsayin tunani mai zurfi, inda ya bukaci a duba takardar da kyau a mayar masa da martani.

Ga cikakken jerin sharudda 19 da Eric Chelle ya gabatar ga hukumar kwallon kafa ta Nijeriya (NFF):

1. Motar alfarma ta (SUV) tare da direba da jami’in tsaro.

2. Gida a cikin unguwa mai tsaro tare da wutar lantarki ta awanni 24 ba tare da katsewa ba.

3. A tanadar mashi da ofishi mai dauke da kayan aiki na zamani.

4. Samar da ingantaccen intanet.

5. Tikitin jirgin sama ga matarshi da yaransa biyu.

6. Samar da na’urar GPS.

7. Samar da kayan aiki masu kyau bisa ga bukatar kocin.

8. Dangane da wasannin sada zumunta, kocin yana da yancin zabar wasannin sada zumunci da tawagar zata buga.

9. Kocin zai shirya yadda atisayen tawagar zai kasance.

10. Kocin zai gudanar da shirye-shirye domin ci gaban matasan yan wasa.

11. Samar wa kocin damar yin tafiya, kallo, da sa ido ga yan wasan Nijeriya dake buga wasa a Turai.

12. Samar wa kocin damar yin tafiya don kallon gasar kwallon kafa ta gida don gano yan wasa wadanda za a saka a cikin tawagar kasar a matakai daban-daban.

13. A daina tsoma masa baki wajen zabar yan wasan tawagar Super Eagles.

14. Hukumar NFF dole ne ta bayar da kwangilar aiki ga mataimakansa.

15. Ana bukatar biyan albashi a ranar 30 ga kowane wata ko kafin ranar 30 ga wata.

16. Karin albashi da alawus kamar yadda tsarin tawagar ya tanada.

17. Bukatar a saka babban hadiminsa a cikin tsarin alawus.

18. Albashin dala $130,000.00 (dala dubu ɗari da talatin) kowane wata, inda zai kunshi sauran mataimakansa.

19. Ganawa ta wata-wata da dukkan masu horar da sauran tawagogin kwallon kafa a kasar.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *