Darussa Daga Ramadan Na (1)
[ad_1]
A cikin watan Ramalana, mumini yana shiga wata babbar makaranta ta tarbiyya wadda take koyar da shi darussa masu zurfi a aikace, ba fatar baki kaɗai ba. Daga cikin manyan darussan da Ramalana ke koyarwa akwai tsayar da salloli na farilla a kan lokutansu, kamar yadda ake tsare azumi daga hudowar alfijir zuwa faɗuwar rana.
Kamar yadda ba ya halatta mumini ya karya azumi kafin lokacinsa, haka nan ba ya kamata ya jinkirta salla ko ya yi sakaci da ita bayan lokacinta. Wannan tarbiyya ce ta girmama lokaci, da koyon tsari da biyayya ga umurnin Allah.
- SAHUR (Falalarsa Da Fa’idojinsa) Na 1
- SAHUR (Falalarsa Da Fa’idojinsa) Na 2
Azumi yana horar da jiki da ruhi hakuri da kamewa, salla kuma tana gyara zuciya da raya zuciya ta hanyar tsayuwa cikin tawali’u a gaban Ubangiji. Saboda haka, idan aka haɗa su biyun, sai su zama cikakkiyar makarantar gyaran mutum gaba ɗayansa, a zahiri da baɗini. Ba abin mamaki ba ne cewa Allah Maɗaukakin Sarki Ya haɗa siffofin masu khushu’i a salla da masu azumi a wuri guda a cikin Alƙur’ani, musamman a Suratul Ahzab aya ta 35, inda Ya lissafo siffofi masu daraja kamar khushu’i, da azumi, da sadaƙa, da kuma tsare mutunci, da kuma yawaita ambatonsa, watau zikiri. Bayan wannan jerin siffofi, sai Ya yi musu alkawarin gafara da lada mai girma.
Wannan aya tana nuna cewa ibada a Musulunci ba ta rabu da tarbiyyar halin ɗan’adam da tsarkake zuciyarsa ba. Khushu’i a salla alama ce ta nutsuwa da jin girman Allah a zuciya; azumi kuma alama ce ta tsoron Sa da biyayya ga dokokinsa ko da babu wanda ke ganin mutum. Idan mutum ya iya kame kansa daga abin da yake so saboda Allah, to hakan shaida ce ta ƙarfin ruhinsa da ingancin imaninsa.
Saboda haka, Ramalana ba wai wata ne na jin yunwa da ƙishirwa kaɗai ba; wata ne na gyaran hali, da tsarkake niyya, da daidaita rayuwa bisa tsarin Allah. Duk wanda ya koyi tsare lokutan sallarsa, ya yi azuminsa da tsoron Allah, ya kuma rayu da khushu’i da zikiri, to ya cika wasu daga cikin siffofin da Allah Ya yaba. Irin wannan bawan ne ake yi wa bushara da gafara da lada mai girma, lada ne wanda ya fi duk wata ni’ima ta duniya daraja.
Abu Razina Nuhu Ubale Ibrahim Paki
[ad_2]
Source link