Ɗan Najeriya ya kashe mahaifinsa, ya yanki ƙannensa da wuƙa a Amurka

[ad_1]



Wani matashi mai shekaru 27, Chukwuebuka Eweni, ya shiga hannun ’yan sanda a birnin New Orleans na ƙasar Amurka, kan zargin kashe mahaifinsa har lahira tare da jikkata ’yan uwansa mata guda biyu a gidansu da ke unguwar Pebble.

Mahaifin matashin malami ne a fannin kimiyyar kwamfuta a Jami’ar Southern ta New Orleans.

Iyayen matashin waɗanda asalin ’yan Najeriya ne, sun bayyana lamarin a matsayin abin mamaki da ban tsoro.

Sun shaida cewar Chukwuebuka na fama rashin lafiyar ƙwaƙwalwa amma bai taɓa aikata wani mummunan abu ba.

Rahotanni sun nuna cewa ɗaya daga cikin ’yan matan da aka jikkata an sallame ta daga asibiti, yayin da ɗayar ke kwance tana samun kumawar likitoci.

Rundunar ’yan sandan New Orleans ta tabbatar cewa Chukwuebuka yana hannu kuma ana duba lafiyarsa, kafin kammala bincike.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:59 na daren ranar 11 ga watan Nuwamba, 2025.

’Yan sanda sun samu kiran agajin gaggawa, inda suka garzaya gidan da lamarin ya auku suka tarar da mahaifin matashin kwance cikin jini, sannan wasu biyu sun ji rauni.

Yanzu dai ana tuhumar Chukwuebuka da laifuka biyu da suka shafi kashe mahaifinsa da kuma ƙoƙarin kashe ’yan uwansa mata guda biyu.

Ofishin Korer na Orleans Parish, zai bayyana musabbabin rasuwar mahaifin matashin bayan kammala binciken gawar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *