Ɗan Majalisar Kano ya tsere bayan an yi masa ihun “ba ma yi” a taron APC
[ad_1]
An yi wa ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Dawakin Tofa/Tofa/Rimin Gado, Tijjani Abdulkadir Jobe, ihun “ba ma yi” a yayin wani taron zaɓen shugabannin jam’iyyar APC da aka gudanar a Ƙaramar Hukumar Tofa da ke Jihar Kano.
Bidiyoyin da suka karade kafafen sada zumunta sun nuna yadda wasu matasa da magoya bayan jam’iyyar suka yi ta ihu da kalaman nuna ƙin amincewa yayin da ɗan majalisar ke jawabi a taron da aka gudanar a mahaifarsa.
Wannan lamari dai ya sanya ɗan majalisar ya cika bujensa da iska yayin da jami’ansa da magoya bayansa suka gaggauta fitar da shi daga wurin domin kauce wa abin da ka iya zuwa ya komo.
A cikin ɗaya daga cikin bidiyon, an ji wani daga cikin taron na cewa, “Wallahi shugabanninmu, akwai abubuwan da ba a gyara ba. Mu mafarauta ba a kula da mu ba.”
Sai dai daga baya hayaniyar ta ƙara ƙamari, inda wasu matasan suka ci gaba da ihu da zagin ɗan majalisar.
Tun a farkon watan nan ne Jobe ya nemi afuwar jama’arsa kan wasu kura-kurai a wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, taron da rahotanni suka ce ya rikiɗe zuwa hargitsi.
Rahotanni na nuni da za a yi zazzafar fafatawa wajen neman kujerar ɗan majalisar wadda aka soma tun gabanin zaɓe mai zuwa, inda manyan ’yan jam’iyyar ke nuna sha’awar tsayawa takara.
Jobe, wanda ke wa’adinsa na biyar a Majalisar Wakilai, na neman wa’adi na shida, lamarin da ake raɗe-raɗin cewa yana hanƙoron samun tikitin kai tsaye bayan dawowarsa jam’iyyar APC.
Wannan ne karon farko da ake ganin Jobe a wani taron jama’a a Tofa tun bayan nasarar da ya samu a zaɓen 2023.
Wani mazaunin yankin, Umar Danladi, ya ce ƙuduri ɗaya kacal Jobe ya gabatar a tsawon kusan shekara 19 da ya shafe a Majalisar, kuma har yanzu ba su soma ganin tasirinsa ba.
Mazabar Dawakin Tofa/Tofa/Rimin Gado dai ta shahara wajen fitar da manyan jiga-jigan siyasa a Kano, lamarin da ke ƙara ɗora wa duk mai neman wakilcinta nauyin gamsar da al’umma.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link