Zaɓen cike gurbi: An kama ’yan daba 100 a Bagwai — INEC
[ad_1]
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta tabbatar da kama aƙalla ’yan daba 100 da ake zargi da tayar da zaune-tsaye a lokacin zaɓen cike gurbi da aka gudanar a Ƙaramar Hukumar Bagwai a Jihar Kano.
Kwamishinan INEC na Jihar Kano, Abdu Zango, ya shaida wa manema labarai a Bagwai cewa jami’an tsaro suna aikin tabbatar da zaman lafiya domin a gudanar da zaɓen cikin lafiya.
“Dukkanin mutanen da muka gani suna kawo matsala an kama su, kuma zaɓen yana tafiya lafiya.
“Na gamsu sosai da yadda komai ke tafiya. Kayan zaɓe sun isa a kan lokaci, kuma yawancin rumfunan zaɓe sun fara aiki tun ƙarfe 8:30 na safe,” in ji shi.
Zango, ya ƙara da cewa an ɗan samu jinkiri a wasu wurare saboda matsalar sufuri da kuma yunƙurin wasu ƙungiyoyi na kawo cikas.
Amma ya ce jami’an tsaro sun shiga tsakani tare da tabbatar da doka da oda.
Ya ce ko da yake ba zai iya gane mutanen da aka kama ba, rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar masa cewa ta kama aƙalla ’yan daba 100 kuma za a gurfanar da su a gaban kuliya.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link