Yadda aka yi zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a Kano

[ad_1]



Dubban Musulmi a Jihar Kano sun gudanar da zanga-zanga a ranar Juma’a domin nuna goyon baya ga Falasɗinawa tare da yin Allah-wadai da hare-haren da ake kai wa Iran.

Yawancin masu zanga-zangar mabiya Shi’a ne.

Sun taru ne bayan idar da sallar Juma’a a Masallacin Fagge da ke birnin Kano.

Masu zanga-zangar sun yi tattaki a manyan tituna ɗauke da tutocin Falasɗinu, Iran da Najeriya.

Sun yi zanga-zangar ɗauke da kwalaye masu rubuta kamar “Free Palestine,” “Death to Israel,” da kuma “We support Iran.”

A yayin zanga-zangar, sun kuma nuna wasu akwatunan gawa guda biyu da aka lulluɓe da tutocin Amurka da Isra’ila.

Sun ɗora hotunan Donald Trump da Benjamin Netanyahu a kan akwatin gawarwakin.

Zanga-zangar ta gudana cikin lumana na kusan awa uku.

Masu zanga-zangar sun fara daga masallacin, suka bi titin Ibrahim Taiwo Road, sannan ƙare a gadar da ke kusa da Ƙofar Nassarawa a titin Zariya.

Da yake jawabi bayan kammala zanga-zangar, Sheikh Sidi Munir Mainasara, ya ce sun shirya zanga-zangar ne domin tunawa da ranar Ƙudus, wadda ake yin ta a ranar Juma’ar ƙarshen watan azumin Ramadan.

Ya ce an shafe sama da shekaru 40 ana gudanar da wannan rana a ƙasashe daban-daban ta hanyar wayar da kai, laccoci da tattaunawa kan batun Falasɗinawa.

A cewarsa, bikin na bana yana da muhimmanci saboda rikicin da ake yi a Falasɗinu, inda mutane da dama suka mutu, wasu suka jikkata, yayin da wasu kuma suka rasa matsugunansu.

Mainasara, ya kuma yaba wa Jagoran addinin Iran, Ali Khamenei, inda ya ce yana daga cikin shugabannin da ke goyon bayan waɗanda ake zalunta a duniya.

Malamin ya buƙaci ƙasashen duniya su ɗauki mataki kan zaluncin da Isra’ila ke yi, tare da sake jaddada buƙatar ’yantar da Falasɗinawa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *