Wata mata ta ƙona farjin ’yarta da wuta kan zargin maita a Bauchi

[ad_1]



Wata mata mazauniyar garin Magama Gumau a Ƙaramar Hukumar Toro, Jihar Bauchi, ta shiga hannun ’yan sanda biyo bayan ƙona farjin ’yarta mai shekaru 10 kacal a duniya, kan zargin maita.

Rahotanni sun nuna cewa matar ta yi amfani da cokali ta hanyar sanya shi a wuta ya yi zafi sannan ta umarci ’ya’yanta biyu suka riƙe yarinyar sannan ta ƙona ta.

Wannan ya jefa yarinyar cikin mawuyacin hali, inda ta ke fama wahalar yin fitsari da bayan gida.

Bayan lamarin ya faru, maƙwabta sun kai ƙarar matar wajen ’yan sanda.

An garzaya da yarinyar zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) domin kula da ita.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Bauchi, CSP Mohammed Ahmed Wakil, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce an kama matar da wasu, ciki har da wata mai maganin gargajiya mai suna Fatima Abdullahi, wadda ta karɓi kuɗin matar sannan ta tabbatar mata cewa yarinyar mayya ce.

A cewar rundunar, lamarin ya faru ne ranar 11 ga watan Satumba, 2025.

Tuni Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Sani-Omolori Aliyu, ya bayar da umarnin a gudanar da bincike, tare da tabbatar da adalci.

’Yan sanda sun kuma ja hankalin iyaye da su daina kai yara wajen bokaye, domin hakan na iya jawo ɓarna maimakon samun waraka.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *