Wani mutum ya yi wa abokin ƙuruciyarsa kisan gilla

[ad_1]



Wani ɗan Najeriya da ke zaune a Turai, Mista Eghosa Osarietinomwan, ya gamu da ajalinsa a hannun tsohon abokinsa na ƙuruciya, Mista Amadin William, a Oben da ke Ƙaramar Hukumar Orhionmwon ta Jihar Edo.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a lokacin shagalin tarewa a sabon gida da mamacin ya shirya a ranar 22 ga Disamba, 2025.

Mamacin ya dawo daga Turai ne domin yin bikin Kirsimeti tare da iyalansa, amma sai aka kashe shi.

Rahotanni sun bayyana cewa wanda ake zargi ya ja mamacin zuwa gefen wata hanya ta daji bayan ya fita domin biyan buƙata, inda ya kai masa hari da adda.

Daga bisani aka garzaya da shi asibiti, inda aka tabbatar da mutuwarsa.

Bayan faruwar lamarin, wanda ake zargi ya tsere daga garin, amma daga baya ’yan sanda suka bi diddigi suka cafke shi a Benin City a ranar 27 ga Disamba.

Hakan ya fusata matasan yankin, inda suka banka wa gidan wanda ake zargi wuta, lamarin da ya jawo ƙarin rikici a ƙauyen.

Mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar Edo, ASP Eno Ikoedem, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce an tsare wanda ake zargi a sashen binciken manyan laifuka na jihar (SCID).

Ta ƙara da cewa an kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu wajen kona gidan bayan kisan.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *