Trump ya shawarci Maduro ya miƙa mulki cikin ruwan sanyi
[ad_1]
Shugaban Amurka Donald Trump ya sake jaddada barazana kan taƙwaransa na Venezuela Nicolas Maduro tare da yi wa shugaban Colombia, Gustavo Petro, hanunka mai sanda.
Yayin wani taron manema labarai da ya shirya ranar litinin da ta gabata a Florida, Donald Trump, ya shawarci Nicolas Maduro da ya mika mulki cikin ruwan sanyi.
Da wani ɗan jarida ya tambayi Trump kan ko matakin Washington nada manufar matsin lamba ga Nicolas Maduro domin ya bar mulki?
Sai ya kada baki ya na mai cewar shi ya san abin da ya dace ya yi, amma ina shawartarsa da ya yiwa kansa zabi mai kyau.
Trump, ya kuma bayyana anniyarsa na cigaba da tsare jirgin ruwan dakon mai mallakin Venezuela da dakarun ƙasar suka tsare ranar 10 ga watan disamban nan a tekun Pacifik.
[ad_2]
Source link