Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori

[ad_1]


Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da sababbin ayyukan da aka yi a jami’ar Ilori a matsayin wasu abubuwan da ake yi na bukukuwan saukar karatu na 40 da za ayi.

Ayyukan sun hada da azuzwa hudu na lacca a sashen kimiyyar zamantakewa da kuma kimiyya yadda za’a iiya da tafiyar da lamurra, ofishin sashen Turanci da Wasan kwaikwayo wanda yake karkashin sashen Fasaha, gine – gine 10 da aka yi wa kwaskwarima,sai sashen labarin kasa da tafiyar da muhalli, yadda aka sake tsara ita jami’ar Ilorin domin tafiya kafada- kafada da takwarorinta na duniya ba ma na Nijeriya kadai ba,da kuma hanyar zuwa cibiyar fasahar koyon wasu abubuwa.

Shugaban kasa Tinubu, wanda mataimakin Shugaban jami’ar fasaha ta gwamnatin tarayya da ke Akure ya wakilta (FUTA), Farfesa Adenike Oladiji ya ce su sabbin ayyukan da aka kaddamar sun nuna a fili yadda tsarin Jami’a yake taimaka wa al’umma.

Ya yi kira ga hukumomi Jami’ar da cewa su kula da tabbatar da abubuwan da aka kaddamar, inda ya kara da cewa shi kudurin wannan gwamnati ya hada ne da tsarin yadda za a tafiyar da bunkasar ilimi, da abubuwan more rayuwa a duk fadin Nijeriya.

Ya ce: “Ayyukan sun nuna yadda manufa da fatar ci gaba da samar da abubuwan da za su bunkasa ci gaban kasa gaba daya. Don haka yana fatan ‘yan Nijeriya za su amince da kudurin da gwamnati take da shi na ‘yan Nijeriya da shi ci gaban Nijeriyar daga cikin kunci zuwa yanayin da za a rika yin godiya.”

Bug da kari Tinubu ya jinjina wa Shugaban jami’ar, Farfesa Wahab Olasupo Egbewole (SAN)da ‘yan tawagarsa wajen maida hankalin da suka yi na bunkasa Jami’ar da kumna kudurinta na muradun ci gaban da ake bukata.

Shi ma anashi jawabin Shugaban Jami’ar Sarkin Katsina, Alhaji. Abdulmumin Kabir Usman, wanda Wazirin Katsina, Sanata Ibrahim Idah ya wakilta, ya nuna jin dadinsa kan irin kokarin da UNILORIN saboda bunkasar ilimi da kumasamar wuraren koyon kaaratu masu kyau da kuma suka dace.

Ya yi ma kallon ayyukan da ak kaddamar a matsayin“ irin abubuwan da ake bukatar gani ke nan”da za su taimakawa lamarin koyarwa, koyo,da kuma bincike, inda ya kara da cewa yadda Jami’ar ta maida hankalinta wajen bunkasa dabarar koyon yin abubuwa zai taimakawa dalibai su tashi da sun koyi abubuwan da zasu yi baya rayuwar da suka yi cikin aji.

A nashi jawabin mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa. Egbewole ya nuna farin cikinsa da godew a Shugaban kasa Tinubu kan yadda ya amince da gaiyar da Jami’ar ta yi ma shi, da kuma taimaka mata wajen tafiyar da bunkasar abubuwan jin dadi.

“Muna nan muna sa ido saboda ci gaban samun abubwan da suke taimakawa ci gaba kwarai da gaske a kowace rana kamar yadda yace yana da amincewa da yardarm ci gaba da samun hakan’’.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *