Tinubu ya buƙaci ’yan Najeriya du daina yi wa ƙasar mummunan fata
[ad_1]
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya roƙi ’yan Najeriya da su daina yin maganganu ɓatancin ga ƙasar.
Ya ce Najeriya ƙasa ce mai girma, mai cike da damar ci gaba.
Shugaban ya yi wannan jawabi ne a daren ranar Talata a Jihar Legas, lokacin da aka sake buɗe Cibiyar Al’adu ta Ƙasa (National Theatre) da aka gyara.
Ya ce dole ne ’yan ƙasa su yi imani da Najeriya kuma su haɗa kai domin gina ta.
“Ku daina yin magana mara kyau game da Najeriya. Mu mutane ne masu alfahari, jarumai, da jajirtattu. Mu gina wannan ƙasa tare, mu sake farfaɗo da ita,” in ji Tinubu.
Ya yaba da arziƙin al’adu da baiwar da Najeriya ke da ita, inda ya bayyana cewa wannan shi ne ɗaya daga cikin manyan ƙarfinta.
Haka kuma ya jinjina wa fitaccen marubuci, Farfesa Wole Soyinka, saboda gudunmawarsa ga adabi da ci gaban ƙasa.
Tinubu ya ce sake farfaɗo da cibiyar alama ce ta ƙarfi da juriyar Najeriya.
Ya ce za ta samar da ayyukan yi, bunƙasa fasaha, da kuma zama cibiyar al’adu a Afirka.
Shugaban ya kuma yaba wa Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, da sauran waɗanda suka bayar da gudunmawa wajen kammala aikin.
Tinubu, ya nuna ƙwarin gwiwa kan tattalin arziƙin ƙasar: “Idan an tafiyar da shi yadda ya dace, arziƙi bunƙasa.
“Ku yi imani da kanku, ku bai wa mutane dama, ku ba su ƙwarin gwiwa. Najeriya ita ce giwar Afirka, kuma ba za ta durƙush3 a zamanina ba.”
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link