Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’adda 3, Sun Ƙwato Makamai A Sakkwato

[ad_1]

Dakarun Rundunar Sojin Ƙasan Nijeriya sun kashe wasu da ake zargin ’yan ta’adda uku tare da ƙwato makamai a wani samame da suka kai a cikin dajin Kadam da ke ƙaramar hukumar Tangaza a Jihar Sakkwato.

Sojojin Bataliya ta 7 ta rundunar sojin ƙasa ce suka gudanar da aikin tare da tawagar farmaki ta 8, ƙarƙashin Operation Fansan Yamma.

  • Saudiyya Ta Rage Samar Da Man Fetur Saboda Matsalar Jigila A Hormuz
  • Gwamna Abba Ya Sauke Shugaban Ma’aikatan Kano Daga Muƙaminsa

A wata sanarwa da Muƙaddashin Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na runduna ta 8, Olaniyi Osoba ya fitar, ya ce sojojin sun fafata da wata ƙungiyar ’yan ta’adda da ke da alaƙa da Lakurawa.

Ya ce samamen ya biyo bayan sahihin bayanan sirri da suka nuna cewa ’yan ta’adda sama da 100 sun taru a cikin dajin Kadam domin kai hare-hare da sace-sace a ƙauyukan da ke kusa da yankin.

“A bisa wannan bayanin sirri, sojoji suka yi gaggawar zuwa wajen domin tare su. An yi arangama da su da misalin ƙarfe 12 na rana,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa an yi musayar wuta mai tsanani, inda ’yan ta’addan suka yi ƙoƙarin kai hari daga baya, amma sojojin suka daƙile su.

Bayan arangamar, sojojin sun ci gaba da bincike a cikin dajin inda suka tabbatar da kashe ’yan ta’adda uku, yayin da ake zargin wasu sun tsere da raunukan harbin bindiga.

Haka kuma sojojin sun ƙwato bindiga ƙirar PKT guda ɗaya, bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu, harsasai 350 na PKT, harsasai 111 masu ɗangon 7.62mm, mujallu uku na bindiga, rediyoyin sadarwa guda biyu, babura uku da kuma wayar hannu guda ɗaya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *