Shugaban APC ya gana da Bala Mohammed kan jita-jitar sauya sheƙarsa zuwa ADC
[ad_1]
Ƙasa da sa’o’i 24 da ziyarar da wasu jiga-jigan jam’iyyar ADC suka kai wa Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, kan yiwuwar komawa jam’iyyarsu, tawagar jam’iyyar APC, ta yi dirar mikiya a jihar.
Tawagar ta haɗa da Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.
Sun tafi kai-tsaye ofishin Gwamnan a Gidan Gwamnatin Bauchi, inda suka yi ganawar sirri da shi.
Da akwai wasu daga cikin manyan jami’an gwamnatin jihar da suka kasance a ganawar, ciki har da Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Abubakar Y. Suleiman, Sakataren Gwamnatin Jihar, Aminu Hammayo, da Shugaban Ma’aikata.
Ko da yake ba a bayyana dalilin ganawar ba, majiyoyi sun nuna cewa ziyarar na da nasaba da yunƙurin hana gwamnan da magoya bayansa ficewa zuwa jam’iyyar ADC.
Idan ba a manta ba a baya-bayan nan gwamnan ya bayyana cewar zai iya ficewa daga PDP sakamakon rikicin cikin gida da ta ke fama da shi.
Ganawar ta ɗauki kusan sa’a guda, amma babu wanda daga cikin tawagar ya yi magana da ’yan jarida bayan ganawar.
Sun koma filin jirgin saman Bauchi, inda daga nan suka wuce Abuja.
Gwamna Bala bai yi wa ’yan jarida ƙarin bayani game da abin da suka tattauna ba.
A baya, gwamnan ya bayyana cewa yana duba yiwuwar ficewa daga jam’iyyar PDP ya koma ADC, wacce yake ganin tana da ƙarfin ƙalubalantar APC a zaɓen 2027.
Ya ƙara da cewa zai yanke shawara ta ƙarshe nan ba da jimawa ba, inda ake sa ran sanarwarsa a hukumance nan da ranar Alhamis, 2 ga watan Afrilu.
“Muna sane da lokacin da ya dace. Komai zai kammala nan da ranar Alhamis domin mu ci gaba da tafiya tare. Za ku ji sahihin bayani daga gare mu,” in ji shi.
Yanzu hankalin jama’a ya karkata zuwa ranar Alhamis, inda ake sa ran gwamnan zai bayyana matsayarsa ta ƙarshe kan jam’iyyar da zai koma tare da magoya bayansa.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link