Shettima Ya Ziyarci Waɗanda Harin Bam Ya Shafa A Maiduguri
[ad_1]
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya ce Gwamnatin Tarayya ta ƙudiri aniyar kawo ƙarshen ta’addanci tare da ɗaukar mataki mai tsauri kan waɗanda ke da hannu a hare-haren da suka faru kwanan nan.
Ya bayyana cewa gwamnati ba wai kawai tana bai wa jami’an tsaro umarni ba ne, har ma tana ƙara samar da kayan aiki da goyon baya domin ƙarfafa yaƙi da ta’addanci.
- Ministan Harkokin Wajen Sin: Babakere Ba Ya Samar Da Mafita
- Sojoji Sun Ƙwato Shanun Sata A Filato
Shettima ya bayyana haka ne a ranar Laraba a Maiduguri yayin da ya ziyarci waɗanda suka jikkata sakamakon fashewar bama-bamai da suka faru ranar Litinin, a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri.
Ya yi Allah-wadai da hare-haren, inda sama da mutum 100 suka jikkata, yayin da sama da 20 suka rasu.
Ya bayyana masu aikata harin a matsayin azzalumai, yana mai cewa babu wani dalili da zai sa a kashe mutane marasa laifi.
Mataimakin Shugaban Ƙasan ya ce ziyarar tasa domin jajanta wa waɗanda suka jikkata da kuma iyalan waɗanda abin ya shafa.
Ya kuma ba su tabbacin cewa gwamnati za ta tallafa musu ta hannun hukumomi kamar NEMA, Hukumar Raya Yankin Arewa maso Gabas, da kuma Gwamnatin Jihar Borno.
Ya samu rakiyar Mataimakin Gwamnan Jihar Borno, Usman Kadafur, da sauran manyan jami’an gwamnati a yayin ziyarar.
Ga hotunan a ƙasa:




[ad_2]
Source link