Saudiyya za da ɗauki ’yan Najeriya aiki a hukumance
[ad_1]
Ƙasar Saudiyya za ta ɗauki ‘yan Najeriya aiki bayan wata yarjejeniya da ƙasashen biyu suka sanya wa hannu ta tsara yadda za a ɗebi ’yan Najeriyar aiki a hukumance.
Yarjejeniyar wacce aka cimma tsakanin ƙasashen biyu ta mai da hankali kan yadda za a deɓi ma’aikatan bisa tsari tare da inganta rayuwarsu a yayin aiki a ƙasar.
Wannan na daga cikin sabbin manufofin ƙasar Saudiyya na cimma burinsu da suka yi wa take da ‘Vision 2030’ da ke da nufin gyara tsarin ma’aikata da kuma bunƙasa tattalin arziƙin ƙasar ta hanyar faɗaɗa hanyoyin samun kuɗi.
Ƙasar ta ce zuwa gaba ƙadan hukumomin da abin ya shafa za su fitar da sharuɗɗa da ƙa’idojin da ake buƙata a cika kafin fara aiki.
Dalilin da Saudiyya ke buƙatar ma’aikatan Najeriya
Ƙasar Saudiyya na ƙara dogaro da ma’aikatan ƙasashen waje domin cike gibi ayyuka a fannoni daban-daban kamar gine-gine, ayyukan hidima, kiwon lafiya, otal-otal da yawon buɗe ido, da kuma harkokin sufuri.
Duk da cewa a baya ma’aikatan ƙasashen Asiya ne suka fi yawa a wajen gudanar da aikace-aikace a Saudiyya, a yanzu ƙasashen Afirka—musamman Najeriya—na samun matsayi a wannan fannin, la’akari da arzikin matasa masu ƙarfi da sauƙin horaswa.
Muhimmancin yarjejeniyar ga Najeriya
Ga Najeriya, wannan yarjejeniya ta zo ne a daidai lokacin da ya dace, la’akari da yadda rashin aikin yi a tsakanin matasa ke ci gaba da ƙaruwa.
Ta hanyar tsara ƙa’idojin ƙaura domin tafiya aiki a Saudiyya, gwamnati na da burin kare haƙƙin ma’aikatan Najeriya a ƙasashen waje, tare da ƙara bunƙasa tattalin arziki da ƙasar ke samu daga aikin yi a ƙetare.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link