Sarkin Musulmi ya ba wa makarantu tallafin N1.3bn a Kebbi
[ad_1]
Gidauniyar Sarkin Musulmi kan Zaman Lafiya da Ci-gaba ta bayar da tallafin kayan da darajarsu ta kai Naira biliyan 1.3 domin tallafa wa makarantun Jihar Kebbi.
Kayan da aka bayar sun haɗa da kujeru da teburan karatu da aka samar karkashin shirin gidauniyar, domin rabawa makarantun jihar a matsayin gudummawa don inganta yanayin ilimi.
Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, wanda ya samu rakiyar Sarkin Argungu, Alhaji Sama’ila Muhammadu Mera ya miƙa kayan ne a hukumance a ranar Litinin ga Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, a Bulasa Warehouse da ke kusa da Birnin Kebbi.
Sarkin Argungu, wanda ya yi jawabi a madadin Sarkin Musulmi, ya bayyana cewa wannan kyauta na cikin manufofin Gidauniyar Sarkin Musulmi na inganta ilimi da walwalar al’umma.
Da yake karɓar kayan, Gwamna Nasir Idris ya bayyana farin cikinsa matuƙa bisa wannan kyautar alheri da kuma yadda Sarkin Musulmi ke ci gaba da goyon bayan ci-gaban ilimi a Jihar Kebbi da ma ƙasa baki ɗaya.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link