Sabon Shirin Sabunta Fata Shi Ne Ƙashin Bayan Ci Gaban Kasa – Gwamna Gombe

[ad_1]

Khalid Idris Doya

Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana shirin Sabunta Fata na Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin salon gwamnatocin da APC ke jagoranta a dukkan matakai don aiwatar da ayyukansu ga ‘yan Nijeriya.

Gwamnan ya yi wannan jawabin ne yayin da ya karbi bakuncin Ko-odinetan Shirin Sabunta Fata na Yankin Arewa Maso Gabas kuma tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, Malam Isa Yuguda, a fadar Gwamnati da ke Gombe.

  • Buƙatar A Sake Duba Sabuwar Dokar Haraji
  • Shari’ar Annabi SAW Ta Fi Ta Sauran Annabawa Sauƙi

Gwamna Yahaya ya yaba da jajircewar gwamnatin APC karkashin jagorancin Tinubu, inda ya bayyana cewa shugabancinsa ya mayar da hankali kan inganta rayuwar ‘yan Nijeriya.

Ya jaddada cewa hangen nesan Gwamnatin Jihar Gombe ya yi daidai da manufar Shugaba Tinubu da kuma manufofin APC, wanda yace suna karfafa Shirin Sabunta Fatan.

“A matsayinmu na Shugabanni a Kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa, yawancinmu gwamnonin APC ne, kamar yadda Gwamnatin Tarayya ita ma ta APC ce. Duk mun yi nasara ne a karkashin manufar sabunta fata, wacce ta kunshi manufofi da ka’idoji da aka gina jam’iyyarmu a kai,” in ji Gwamnan.

Ya ce shirin wani dandamali ne da gwamnatin APC ke amfani da shi wajen aiwatar da manufofi da tsare-tsarenta zuwa fa’idoji na zahiri ga jama’a.

Ya kara da cewa kafa kwamitoci daban-daban da aka yi ya karfafa kudurin jam’iyyar na tabbatar da dorewar shugabanci a dukkan matakai.

Da yake tsokaci kan yanayin siyasar kasar nan, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana kwarin gwiwa game da karuwar karbuwar da jam’iyyar APC ke samu a fadin kasar nan.

Gwamnan ya yi kira ga ‘yan jam’iyyar da masu ruwa da tsaki su ci gaba da mai da hankali, su fuskanci kalubalen dake tasowa cikin himma da kuma tabbatar da cewa Shirin Sabunta Fatan ya isa kowane lungu na kasar nan.

Da yake jawabi tun farko, Malam Isa Yuguda ya ce Shirin na Sabunta Fata, Yuguda ya bayyana shi a matsayin cikakken shiri dake nufin cika alkawuran Shugaba Tinubu na inganta rayuwar talakawan Nijeriya.

Ya amince da sukar da gwamnatin ke fuskanta amma ya ce ‘yan asa da yawa ba su san kalubalen da gwamnatin ta gada ba, ciki har da cire tallafin mai, da raguwar asusun ajiyar kasashen waje da kuma karuwar basussukan cikin gida.

A cewar Yuguda, yanzu shirin zai mayar da hankali kan wayar da kan ‘yan Nijeriya game da manufofin gwamnati, da sauye-sauye da shirye-shiryen ci gaba, yayin da zai kasance dandamalin damawa da jama’a da tallafa musu.

“Wannan shiri ba na raba shinkafa ko gari bane. Ya hada da horar da jama’a kan kananan kasuwanci da sana’o’i da tabbatar da cewa ana sayan kayayyakinsu don kar su yi asara. Manufarmu ita ce tallafawa kimanin mutane 1,000 a kowace gunduma a duk fadin kasar nan. Ko da kaso 50 cikin dari aka cimma to an samu babbar nasara,” in ji shi.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *