Sabon haraji zai jefa ’yan Najeriya cikin baƙar wahala — Peter Obi
[ad_1]
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, ya yi gargaɗin cewa sabon tsarin haraji da Najeriya ta fara amfani da shi zai ƙara tsananta wahalar rayuwar ’yan ƙasa ke ciki.
Ya ce ba za a samu ci gaba a ƙasa ba ta hanyar ƙaƙaba wa talakawa haraji.
A wata sanarwa da ya wallafa a ranar Juma’a, Obi ya ce dole ne tsarin haraji ya kasance na adalci, gaskiya da kuma kula da jin daɗin jama’a.
Ya bayyana cewa shugabanni na gari sukan gina amana ta hanyar gaskiya da bayyana komai a fili ga al’umma.
“Ba za ka iya fita daga talauci ta hanyar ƙaƙaba haraji ba; sai dai ta hanyar samar da abin yi. Haraji a kan talakawa yana ƙara jefa su cikin wahala,” in ji Obi.
Obi ya kuma nuna damuwa kan rahotannin da ke nuna matsaloli a tattare da dokokin haraji.
Ya bayyana cewa bai dace a tilasta wa ’yan ƙasa biyan karin haraji ta hanyar da ba ta fayyace komai ba.
Ya ce dole ne a bi doka tare da sanar da jama’a a fili kan yadda komai ke ƙunshe cikin dokokin.
“Babu wani abun alfahari a samun ƙarin kuɗin shiga na gwamnati alhali jama’a na ƙara faɗa wa cikin talauci,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa a lokuta da dama ana buƙatar ’yan Najeriya su biya haraji ba tare da fahimtar yadda za a yi amfani da kuɗin ba ko ganin amfaninsa a rayuwarsu ba.
A cewarsa, rashin bayyana gaskiya kan haka na rage amincewa tsakanin gwamnati da jama’a.
Obi, ya ce ya kamata gwamnati ta mayar da hankali wajen ƙarfafa ƙananan da matsakaitan ’yan kasuwa domin samar da ayyukan yi, ƙara kuɗin shiga, da faɗaɗa tushen haraji.
Ya kammala da kira ga samar da tsarin haraji na gaskiya da zai kula da talakawa tare da ƙarfafa haɗin kai da ci gaban ƙasa.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link