Rundunar Sojin Nijeriya ta cafke jami’anta 16 kan saɓa ƙa’idar aiki
[ad_1]
Rundunar sojin Nijeriya ta sanar da cafke wasu manyan jami’anta guda 16 kan zarginsu da rashin ɗa’a da kuma saɓa ƙa’idar aiki.
Darekan yaɗa labarai na hedikwatar tsaron soji, Birgediya Janar Tukur Gusau ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa ta musamman da ya fitar a ranar Asabar.
Duk da cewa sanarwar ba ta bayyana sunayen jami’an da aka kama ba, sai dai ta ce binciken da aka gudanar ya danganta laifuffukan su da gaza cin jarabawar samun ƙarin girma da kuma wasu dalilai na daban.
Kakakin sojin ya ce ana tsare da waɗannan jami’ai saboda tuhumar da ake musu, kuma tuni wasu daga cikin su suka fara fuskantar tambayoyi daga masu bincike kamar yadda dokokin soji suka tanada.
Gusau ya ce da zarar an kammala bincike za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotun soji kamar yadda doka ta tanada.
Kazalika, ya jaddada cewar rundunar sojojin ƙasar ba za ta lamunci duk wani yunƙuri da zai ɓata mata suna ba, ko kuma yi mata zagon ƙasa kamar yadda dokar ƙasa ta sanya su a ƙarƙashin dimokuradiyya.
Kakakin ya ce sojojin Najeriya za su ci gaba da gudanar da ayyukan su kamar yadda dokar ƙasa ta tanada.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link