Ranar Hausa ta duniya: Za a yi gagarumin biki a fadar Sarkin Daura

[ad_1]



Gwamnatin jihar Katsina ta ce shirye-shirye sun kankama domin bin sahun sauran sassan duniya a yayin bikin Ranar Hausa ta Duniya a za ake gudanarwa ranar 26 ga watan Agustan kowacce shekara.

Shugaban Hukumar Kula d Tarihi da Al’adu ta jihar, Dr Kabir Ali-Masanawa ne ya bayyana hakan yayin wani jawabi ga manema labarai a Katsina ranar Talata.

Ya ce za a yi taron ne a Fadar Sarkin Daura da ke jihar, kuma ana sa ran manyan baki daga kasashe akalla 24 za su halarta.

Masanawa ya ce wannan shi ne karo na farko da gwamnati ta shiga cikin shirya bikin, inda ya ce hatta Gwamnan jihar, Dikko Umaru Radda ya tsaya tsayin daka wajen ganin bikin ya yi nasara.

Shugaban ya ce ranar na fito da tarihi da al’adun Hausawa a fadin duniya, wadanda suka warwatsu a kasashen duniya daban-daban.

Ya kare da cewa, “Kwanan nan mun ziyarci Fadar Sarkin Daura inda muka jaddada masa alfaharin da muke yi da harshen Hausa.

“Ana sa ran a bana, akwai akalla kasashe 24 da za su halarci bikin na Daura,” in ji shi.

Shugaban hukumar ya kuma ce bikin zain una al’adun Hausawa ta hanyar kade-kade da raye-raye da tufafi da abincin Hausawa.

Daga nan sai ya baki masu shirin shiga jihar tabbacin cewa akwai zaman lafiya kuma suna kokari wajen bunkasa tsaro, ta yadda jihar za ta ci gaba da zama wajen yawon bude ido ga baki.

Daga cikin kasashen da ake has ashen zuwan bakin har da Burtaniya da Amurka da Saudiyya da Ghana da kuma kasar Netherlands, a karon farko.

Kiyasi dai ya nuna Hausa shi ne yare na 11 da aka fi amfani da shi a duniya inda yake da masu amfani da shi sama da miliyan 150.

An dai fara bikin ranar ne a shekara ta 2015 kuma duk shekara akan gudanar da babban taro a sassa daban-daban na duniya.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *