NNPP: Mabiya Kwankwasiyya sun gindaya sharuɗa kafin bin sahun Gwamnan Kano

[ad_1]



Wasu ƙungiyoyin matasan Kwankwasiyya a Jihar Kano, sun ce a shirye suke su mara wa Gwamna Abba Kabir Yusuf baya, bayan ficewarsa daga jam’iyyar NNPP, matuƙar gwamnatinsa za ta sanya matasa cikin harkokin mulki.

Gwamna Abba, ya fice daga jam’iyyar NNPP a ranar Juma’a, inda ya ce rikicin cikin gida da na shugabanci ne suka tilasta masa ɗaukar matakin.

Ya ce waɗannan matsaloli sun raba kan ’ya’yan jam’iyyar tare da raunana haɗin kai.

Da yake magana a wajen taron matasa a Kano, ƙungiyoyin sun ce ba su da matsala da gwamnan a matsayinsa na mutum.

Sai dai suna da ƙorafi kan yadda aka ware su wajen yanke shawara da shirye-shiryen gwamnati.

“A shirye muke, mu tafi tare da Gwamna Abba Kabir Yusuf idan gwamnati da gaske za ta saka matasa a harkokin mulki,” in ji Aminu Abdullahi, wanda aka fi sani da Alhaji Warkal.

Ya ce matasa da dama da suka yi aiki tuƙuru domin nasarar tafiyar Kwankwasiyya da jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023 yanzu an yi watsi da su.

“Waɗannan matasa sun sadaukar da lokacinsu da ƙarfinsu domin kawo gwamnati, amma bayan samun nasara ba a shigar da su cikin shirye-shirye ko shawarwarin da suka shafe su ba,” in ji shi.

Abdullahi ya ƙara da cewa shigar da matasa cikin harkokin mulki na da matuƙar muhimmanci wajen rage takaici, aikata laifuka da tashin hankali a cikin al’umma.

Ya jaddada cewa matsayar matasan ta samo asali ne daga buƙatunsu, ba matsin lambar siyasa ba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *