Natasha Ta Zargi Akpabio Da Sanya Jami’an Tsaro Su Ƙwace Mata Fasfo A Filin Jirgin Saman Abuja

[ad_1]


Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan daga Kogi ta Tsakiya, ta zargi Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da bai wa jami’an hukumar shige da fice, umarnin ƙwace mata fasfo a filin jirgin sama da safiyar Talata.

A wani faifan bidiyo da ta wallafa a Facebook, Sanatar ta bayyana cikin fushi yayin da take cece-kuce da jami’an hukumar, inda ta ce sun riƙe mata fasfo na tsawon minti 20.

“Akpabio ne ya umarce su da su hana ni tafiya. Wannan ba daidai ba ne,” in ji ta.

Natasha ta ce ba wannan ne karon farko da aka taɓa yin irin haka da ita ba, inda ta bayyana cewar Akpabio ya sha zarginta da ɓata wa ƙasa suna duk lokacin da ta fita ƙasashen waje.

Ta kuma bayyana cewa babu wani umarnin kotu da ya halatta hakan, tare da tunatar da jami’an cewa Shugaba Bola Tinubu ya taɓa umartar Akpabio da ya dakatar da duk wasu abubuwa da ake yi mata.

Bayan shafe lokaci, wani jami’in hukumar shige da fice ya dawo mata da fasfo ɗinta.

Duk da haka, Natasha ta ci gaba da nuna ɓacin ranta.

“Da ban yi bidiyon kai-tsaye ba, da ba za su dawo da min fasfo ba.”

A halin da ake ciki, ofishin Akpabio da Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (NIS) ba su fitar da wata sanarwa ba game da lamarin.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *