Muna duba yiwuwar kammala yaƙin Iran — Trump

[ad_1]



Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce gwamnatinsa na duba yiwuwar “kammala” hare-haren soji da ake kai wa Iran, yana mai cewa sun kusa cimma manufofinsu.

Trump ya bayyana hakan ne a ranar Jumma’a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafin Truth Social.

Ya ce: “Mun kusa cim ma muradunmu, don haka muna duba yiwuwar kammala ayyukan da sojojinmu ke yi a Gabas ta Tsakiya kan Iran.”

Ya ƙara da cewa ya kamata sauran ƙasashen duniya su ɗauki alhakin kare Mashigar Hormuz saboda muhimmancinta, yana mai cewa Amurka ba za ta ci gaba da ɗaukar nauyin hakan ita kaɗai ba.

Tashin hankali ya ƙaru a yankin tun bayan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar a Iran ranar 28 ga Fabrairu, wanda rahotanni suka ce sun yi sanadin mutuwar sama da mutum 1,300.

Iran ta mayar da martani da harba makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa kan Isra’ila da wuraren Amurka a ƙasashen Larabawa, lamarin da ya ƙara tsananta rikicin.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *