Mun kashe mayaƙan ISWAP 8, wasu 11 sun miƙa wuya — Sojoji

[ad_1]



Sojojin rundunar Operation Haɗin Kai sun kashe mayaƙan ƙungiyar ISWAP takwas a wani artabu tsakanin ƙauyukan Sojiri da Kayamla a Jihar Borno.

Kakakin rundunar, Laftanar-Kanar Sani Uba, ya ce sun yi artabu da mayaƙan ne bayan samun bayanan sirri, inda suka kashe ’yan ta’adda takwas da kuma ƙwato bindigogi ƙirar AK-47.

Haka kuma, dakarun rundunar Operation DESERT SANITY V, sun ci gaba da ragargaza a yankin Azir-Wajiroko, inda suka tilasta wa mayaƙan ƙungiyar 11 miƙa wuya tare da makamansu.

Tun da farko, a ranar 9 ga Janairu 2026, sojoji sun gudanar da ayyukan sharar fage a a Bulaagalda, inda suka lalata sansanonin ’yan ta’adda da dama a Dagumba, Bonne, Yaganari, Gosuri da Umchile, ciki har da sansanonin Abu Nazir da Abu Ahmed.

Uba ya ce, sojojin sun rushe gine-ginen da ke taimakawa wajen ayyukan ’yan ta’addan tare da lalata wasu muhimman kayayyakinsu sannan suka ƙwato makamai da tutocin ’yan ta’adda.

Haka nan hare-haren da aka kai a yankunan Yale da Bula Gaida sun tilasta wa ’yan ta’adda tserewa, inda aka ƙwato makamai, harsasai da kuma bindiga mai sarrafa kanta.

Uba ya ce sojojin sun ci gaba da “dagewa wajen ci gaba da kai hari don wargaza hanyoyin sadarwar ’yan ta’adda da kuma dawo da zaman lafiya mai ɗorewa,” a yankin.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *