Me haɗewar Kwankwaso da Gawuna ke nufi a Kano?

[ad_1]



Tsohon ɗan takarar Gwamnan Jihar Kano na Jam’iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna, ya ziyarci tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, a gidansa da ke titin Miller Road, Kano, a daren Litinin, 30 ga Maris, 2026.

Ziyarar ta zo ne ’yan sa’o’i bayan Kwankwaso ya sauya sheƙa zuwa Jami’yyar ADC, washegarin da ya sanar da ficewarsa daga Jam’iyyar NNPP nan take domin shirya wa babban zaɓen shekarar 2027.

Kwankwaso ya bar NNPP ne kwana ɗaya bayan ficewar Gawuna daga Jam’iyyar APC mai mulki a matakin ƙasa da kuma Jihar Kano.

’Yan makonni ke nan kuma bayan tashin ƙurar da ta turnuƙe fagen siyasar Kano, sakamakon yadda tsohon yaron Kwankwaso na siyasa, Gwamnan Jihar Kano mai ci, Abba Kabir Yusuf, ya juya masa, ya sauya sheƙa daga NNPP zuwa APC.

Ziyarar Gawuna ga Kwanakwo ta tayar da ƙura kan matakin siyasa na gaba da tsohon mataimakin gwamnan zai ɗauka da kuma tasirin hakan a yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.

Ko da yake ba a bayyana cikakken abin da suka tattauna ba, ana ganin hakan ba zai rasa nasaba da sauye-sauyen da ake yi a fagen siyasar Kano ba gabanin babban zaɓen da za gudanar ƙasa da shekara guda daga yanzu.

Aminiya ta ruwaito cewa a ranar Litinin da aka yi wannan ganawar ce Kwankwaso ya sauya sheƙa zuwa ADC washegarin da ya sanar da ficewarsa daga NNPP nan take.

A ranar Litinin ɗin kuma Gawuna ya fice daga APC, bayan ya ajiye muƙaminsa na Shugaban Bankin Gidaje na Kasa a ranar Asabar.

Tarihi zai maimaita kansa

Tuni aka fara hasashen haɗewar jagororin siyasar biyu a ADC a shirye-shiryen zaɓen 2027 da niyyar kayar da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na APC da kuma Gwamna Abba, wanda ya juya wa Kwankwaso baya.

Kwankwaso ya kasance ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP a zaɓen 2023 kuma har yanzu yana da wannan burin a ADC, jam’iyyar da ake ganin Gawuna zai haɗe da shi da sauran manyan ’yan adawa.

Da taimakon Kwankwaso a NNPP a zaɓen 2023, Abba da tsohon mataimakinsa, Kwamred Aminu Abdulsalam suka, ya kayar da ’yan takarar APC, wato Gawuna da Murtala Garo, waɗanda ke da goyon bayan babban abokin adawar Kwankwaso kuma gwamna mai ci a lokacin, Abdullahi Umar Ganduje.

Tun bayan nasarar Abba zaɓen da kafa sabuwar gwamnatin APC a matakin ƙasa ake ƙishin-ƙishin cewa tana ƙasa tana dabo, inda ake zargin an daƙile Gawuna a APC.

A ɗaya ɓangaren kuma, bayan sauya sheƙar Gwamna Abba zuwa APC kuma, mataimakinsa, Aminu Abdulsalam, ya juya masa baya ya ƙi bin sa, lamarin da ya kai ga yunƙurin tsige Kwamred, har ta kai ga daga bisani ya yi murabus.

Yanzu da ake ganin yiwuwar komawar Gawuna ɓangaren Kwankwaso bayan haɗewar Abba da Ganduje a APC, ana hasashen yiyuwar ADC ta tsayar da Gawuna da Aminu Abdulsalam domin fafatawa da Gwamna Abba a 2027.

Idan hakan ta tabbata, zaɓen Gwamnan Jihar Kano ɗauki hankali matuƙa, domin kuwa, tsofaffin abokan adawa ne za su maimaita gogayyar da suka faro a zaɓen 2023, inda su Gawuna ke neman rama kayen da suka sha a hannun Abba, a yayin da shi kuma zai nemi ya ƙara kayar da su domin ya samu wa’adin mulkin na biyu.

Wannan na nufin tsoffafin ’yan gidan Kwankwaso da ’yan Gidan Ganduje za su sake karawa da juna, amma a wannan karon kowannensu zai ya tunkari ɓangaren tsohon uban gidansa ne.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *