Matsalar kashe-kashe a Nijeriya ba ta da alaƙa da addini — Femi Kayode
[ad_1]
Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Cif Femi Fani-Kayode, ya bayyana cewa matsalar kashe-kashen da ake fama da su a sassa daban-daban na ƙasar nan ba ta da alaƙa da addini, illa dai ayyukan miyagu da ke kashe Musulmi da Kirista ba tare da la’akari da bambancin addini ba.
Fani-Kayode ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi a matsayin bako mai jawabi a taron cika shekaru 35 da kafuwar Cocin Anglican da ke garin Kafanchan a Jihar Kaduna.
Tsohon Ministan ya ce lokaci ya yi da ‘yan Najeriya za su dawo daga rakiyar mutanen da ke amfani da addini wajen raba kan al’umma, yana mai cewa masu kashe Kiristoci su ne dai ke kashe Musulmi.
Ya buƙaci mabiya addinan biyu da su rungumi zaman lafiya, haɗin kai da fahimtar juna, tare da guje wa duk wani yunƙurin na kawo rarrabuwa ko tashin hankali.
A nasa ɓangaren, Babban Mai Shari’a na Jihar Kaduna, Barista James Kanyip, wanda ya wakilci Gwamnan Jihar, Sanata Uba Sani, ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar na ci gaba da kare ‘yancin addini da tabbatar da haɗin kai da shugabannin addinai, musamman masu wa’azin zaman lafiya da jituwa.
Shi ma Bishop Markus Dogo na Cocin Anglican da ke Kafanchan, ya bayyana irin ayyukan jin ƙai da cocin ya gudanar cikin shekaru 35, ciki har da gina makarantu, asibitoci da cibiyoyin koyon sana’o’i don tallafa wa marasa galihu.
Haka kuma, Sanatan Kaduna ta Kudu, Barista Sunday Marshall Katung, wanda ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Jema’a da Sanga, Hon. Daniel Amos ya wakilta, ya yaba wa Gwamna Uba Sani bisa yadda yake tafiyar da mulki cikin adalci da rashin nuna wariya ga kowane ɓangare na jihar.
Taron ya samu halarci manyan shugabannin addini, na siyasa da na al’umma, inda suka jaddada muhimmancin zaman lafiya da haɗin kai a matsayin ginshiƙai na ci gaban Najeriya.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link