Matatar Dangote Ta Sake Ƙara Farashin Fetur Zuwa ₦1,175
[ad_1]
Ana hasashen farashin kayayyaki da ayyuka a faɗin Nijeriya zai ci gaba da ƙaruwa bayan wani sabon ƙarin farashin fetur, bayan da matatar man fetur ta Dangote ta kara farashi zuwa N1,175 kan kowace lita, wanda ya zama karo na uku da aka ƙara farashin cikin mako guda.
Sabon sauyin farashin ya zo ne sa’o’i kaɗan bayan jaridar The PUNCH ta yi hasashen cewa, farashin fetur na iya ƙaruwa karo na uku cikin mako guda, bayan dakatarwar wucin gadi da matatar ta yi kan sayar da fetur a ranar Lahadi.
Matatar ta sanar da ‘yan kasuwa sabon ƙarin farashin ne a ranar Litinin, inda ta ɗaga farashin zuwa N1,175 kan kowace lita, daga N995 kan kowace lita da aka sanar a ranar Juma’a. Wannan na nufin an samu ƙarin N180.
[ad_2]
Source link