Kotu Ta Sake Hana PDP Gudanar Da Babban Taronta Na Ƙasa
[ad_1]
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta sake dakatar da jam’iyyar PDP daga gudanar da taronta na ƙasa na shekarar 2025 da aka shirya yi a Ibadan, Jihar Oyo, daga ranar 15 zuwa 16 ga watan Nuwamba.
Alƙalin kotun, Mai shari’a Peter Lifu, ya kuma umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ka da ta amince da sakamakon taron idan aka gudanar da shi.
Wannan umarni ya biyo bayan ƙarar da tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya shigar, inda ya zargi jam’iyyar PDP da hana shi siyan fom ɗin neman takarar shugabancin jam’iyyar.
Mai shari’a Lifu ya yanke hukuncin cewa PDP ta kasa bin dokokin da suka dace wajen shirya taron, ciki har da rashin wallafa jadawalin taron kamar yadda doka ta tanada.
Ya ce Lamido zai shiga mawuyacin hali idan aka yi taron ba tare da an bashi damar tsayawa takara ba.
Alƙalin ya jaddada cewa wajibi ne a bi doka da oda domin kare tsarin dimokuraɗiyya, inda ya yi gargaɗin cewa karya doka na iya jefa ƙasa cikin ruɗani.
A baya, Mai shari’a James Omotosho, ya taɓa bayar da irin wannan umarni, inda ya dakatar da PDP da INEC daga gudanar ko amincewa da sakamakon taron saboda rashin bin ƙa’idojin doka, ciki har da gaza bayar da sanarwar kwanaki 21 kafin gudanar da taron kamar yadda doka ta tanada.
[ad_2]
Source link