Kano Pillars ta samu nasara karon farko a wasan baƙunta a bana

[ad_1]



Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta samu nasara karon farko a wasan baƙunta bayan doke Nasarawa United da  ci 1-0 a wasan mako na 20 na babbar gasar tamaula ta Najeriya.

Wasan da aka buga a birnin Lafia, ya bai wa Pillars damar samun maki uku na farko a wajen gida cikin duk wasanni 20 da ta buga a bana.

Dan wasan gaban Pillars, Chidozie Okorie ne ya zura ƙwallon a minti 49 wadda ya jefa da taimakon Rabiu Ali Pele, bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

Kafin wannan wasan dai, Nasarawa United ta buga wasanni 10 ba tare da an doke ta a gida ba.

Alƙaluma sun nuna cewa wannan nasarar da Kano Pillars ta samu ta ba ta damar matsawa zuwa mataki na 13 da maki 23 cikin wasanni 20 da ta buga.

Ita kuwa Nasarawa United ta yi ƙasa zuwa mataki na 5 da maki 33 cikin wasanni 20 da suka buga a bana.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *