Jihar Kwara Ta Rufe Makarantu A Ƙananan Hukumomi 4
[ad_1]
Gwamnatin Jihar Kwara ta bayar da umarnin rufe makarantu a kananan hukumomi hudu na Jihar a daidai lokacin da ake fama da rashin tsaro a wasu al’ummomin jihar.
Ƙungiyar Malamai ta Nijeriya (NUT), reshen Jihar Kwara ce, ta bayyana sanarwar a madadin gwamnati a ranar Laraba.
A cewar wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba kuma LEADERSHIP ta samu, shugaban NUT, Yusuf Agboola, ya sanar da rufe makarantu a kananan hukumomin Isin, Irepodun, Ifelodun, da Ekiti.
Agboola ya bayyana cewa, matakin ya biyo bayan umarni mai tsauri daga Ma’aikatar Ilimi da Ci gaban Jama’a bayan da gwamnati ta nuna damuwa game da sabbin barazanar tsaro a yankin Kudancin Kwara.
In ba a manta ba, LEADERSHIP Hausa ta rahoto cewa, ‘yan bindiga sun kai hari kan reshen Cocin Christ Apostolic (CAC) a Oke Isegun a cikin al’ummar Eruku, karamar hukumar Ekiti ta Jihar Kwara a ranar Talata, 18 ga Nuwamba, 2025, inda suka kashe akalla masu ibada biyu tare da sace sama da mutane 35, ciki har da faston cocin.
[ad_2]
Source link