Jama’a sun koka kan rashin kammala aikin titi a Kafanchan




Ƙungiyar Ci Gaban Masarautar Jama’a (JEDA), ta roƙi Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, da ya kammala manyan titunan Birnin Kafanchan, wanda aikin ya tsaya tun zamanin Nasir El-Rufai.

Muƙaddashin shugaban ƙungiyar, Ahmad Usman Husain, ya ce waɗannan tituna na da muhimmanci wajen bunƙasa tattalin arziki da rayuwar yau da kullum a Kudancin Kaduna.

Ya ƙara da cewa abin takaici ne a ce ba a haɗa titunan Kafanchan cikin jerin sabbin ayyukan da gwamnan ya ƙaddamar ba, duk da cewa ya yi alƙawarin kammala su a lokacin yaƙin neman zaɓe.

Ƙungiyar ta bayyana Kafanchan a matsayin cibiyar kasuwanci da zamantakewar al’ummar Kudancin Kaduna.

Ta ce titunan na muhimmanci wajen harkokin kasuwanci, lafiya, ilimi da hulɗar jama’a.

JEDA, ta yi kira ga gwamnan da ya cika alƙawuransa, ta hanyar adalci wajen rabon ayyukan ci gaba.

Sannan ya tabbatar da cewa al’ummar Masarautar Jama’a ba a bar su a baya ba.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *