Iran ta naɗa Zolghadr magajin Larijani
[ad_1]
Fadar shugaban ƙasar Iran ta naɗa tsohon kwamandan soja, Mohammad Bagher Zolghadr, a matsayin sabon sakataren hukumar tsaron ƙasar, domin maye gurbin Ali Larijani da aka kashe a hare-haren haɗin gwiwar Amurka da Isra’ila.
Sanarwar naɗin ta fito ne daga mataimakin kakakin ofishin shugaban ƙasar Iran, Seyyed Mehdi Tabatabaei, inda aka bayyana cewa sabon shugaban tsaron zai jagoranci harkokin tsaro a daidai lokacin da ƙasar ke fama da yaƙi.
Mohammad Bagher Zolghadr tsohon babban jami’i ne a rundunar juyin-juya-hali (IRGC), inda ya kai muƙamin birgediya janar, sannan ya riƙe muƙamai daban-daban a fannin soja da tsaro.
Ya taɓa jagorantar sashen horaswa na IRGC a shekarun 1980, sannan ya shugabanci sashen harkokin yaƙi, tare da zama mataimakin babban hafsan rundunar sojin Iran kan harkokin Basij.
Haka kuma, ya taɓa zama mataimakin ministan tsaro da kuma mataimakin shugaban ɓangaren dabarun shari’a a fannin gwamnati.
Naɗin nasa na zuwa ne a lokacin da ake ganin Iran na ƙoƙarin ƙarfafa tsarinta na tsaro, musamman bayan kashe manyan jami’anta cikin makonnin baya-bayan nan.
A wani jawabi, wani babban kwamandan sojin Iran Manjo-Janar Ali Abdollahi Aliabadi ya jaddada cewa dakarun ƙasar za su ci gaba da yaƙi har sai sun samu cikakkiyar nasara, yana mai cewa za su kare martaba da ’yancin ƙasar ba gudu babu ja da baya.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link